Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce ta bankado shirin da wasu ke yi don bata sunanta da na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sakamakon tsare Godwin Emefiele, shugaban babban bankin kasar da aka dakatar daga aiki.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta ce jami'anta sun gano cewa wasu mutane da kungiyoyi na shirin gudanar da zanga-zanga a wasu sasan kasar da zummar "bata sunan" hukumar da gwamnati bisa "dakatarwa da kuma yin bincike kan Mr Godwin Emefiele."
"Wadannan kungiyoyi za su taru a sassa daban-daban na Abuja da Lagos a makonni masu zuwa dauke da kwalaye masu rubutun da ke nuna gwamnati a matsayin mara kyau sannan su yi kira da a saki Emefiele nan take," in ji sanarwar da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar.
DSS ta kara da cewa tana sane da yadda aka dauki nauyin wasu mutane suke rubuce-rubuce da sharhi a soshiyal midiya da ma sauran kafafen sadarwa don cimma burinsu.
Ta kara da cewa ta gano masu son yin kutse cikinta don yin amfani da "ma'aikata bara-gurbi" da zummar bata sunan shugabanninta.
A makon jiya ne wata kotu ta umarci DSS ta bai wa iyalan Emefiele damar ganawa da shi, amma a sanarwar tata hukumar ta ce tuni ta bai wa "iyalan Emefiele, likitoci da duk mutanen da suka dace damar ganawa da shi, tun ma ranar da aka tsare shi, kafin kotu ta umarci a yi hakan".
A makon jiya DSS ta ce Mr Emefiele ya shiga hannunta jim kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga shugabancin babban bankin kasar sannan ya bukaci a yi bincike a kansa.
Kazalika an umarce shi ya mika ragamar tafiyar da bankin a hannun mataimakinsa Mr. Folashodun Adebisi Shonubi.
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa 'yan kasar cikin mawuyancin hali sannan 'yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da zummar cin zarafinsu.
An nada Emefiele a matsayin shugaban Babban Bankin Nijeriya a 2014 bayan an dakatar da Sanusi Lamido Sanusi.