Diphtheria: Kungiyar Médecins sans Frontières na so a kara mayar da hankali kan rigakafin makarau a Nijeriya

Diphtheria: Kungiyar Médecins sans Frontières na so a kara mayar da hankali kan rigakafin makarau a Nijeriya

Kungiyar ta jaddada cewa akwai bukatar fito da tsari mai tsawo na rigakafin ta yadda za a gudanar da shi a jihohi da kananan hukumomi a Nijeriya ga yara.
Cutar ta kashe kusan mutum 600 a Nijeriya tun bayan barkewarta. / Hoto:Getty Images

Kungiyar Likitoci ta Médecins sans Frontières ta yi kira tare da karfafa gwiwar kungiyoyin lafiya da gwamnatin Nijeriya domin gudanar da rigakafin cutar makarau.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata inda ta jaddada cewa akwai bukatar fito da tsari mai tsawo na rigakafin ta yadda za a gudanar da shi a daukacin jihohi da kananan hukumomin Nijeriya ga yara.

Tuni dama aka soma shirin gudanar da rigakafin cutar a Nijeriya karkashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.

Za a gudanar da rigakafin ne a matakai uku a jihohi 14 na kasar wadanda suka hada da jihohin Katsina da Bauchi da Borno da Gombe da Jigawa da Kaduna da Kano da Yobe da Legas da Nasarawa da Osun da Filato da Zamfara da kuma Abuja babban birnin kasar.

A cewar kungiyar, Nijeriya na fuskantar gagarumar matsala ta cutar ta makarau inda ake zargi kusan mutum 17,000 sun kamu da ita, kusan mutum 600 kuma sun rasu.

Labari mai alaka: Diphtheria: Cutar makarau ta bulla a wasu kananan hukumomin Kaduna

Kungiyar ta kuma bayyana cewa a jihar Kano kadai, mutum 12,000 ake tunanin sun kamu da cutar, kuma kashi 70 cikin 100 na wadanda aka kwantar da su a asibiti ba a yi musu rigakafin cutar ba, abin da ke nuna karancin rigakafi a jihar.

Kungiyar ta Médecins sans Frontières ta kuma ce abin damuwa ne matuka kididdigar da ake da ita wadda ke nuna karancin gudanar da rigakafin a Arewa Maso Yammacin Nijeriya.

Ta ce a Sokoto, kashi 6 cikin 100 kadai aka yi wa rigakafin sai a Zamfara kaso 18 cikin 100 aka yi wa rigakafin sai kuma jihar Katsina kashi 18.

Kungiyar ta ce lamarin ya fi kamari a Arewa Maso Gabashin Nijeriya inda kaso 15 cikin 100 kadai na wadanda aka samu sun kamu da cutar aka yi wa cikakken rigakafin cutar.

TRT Afrika da abokan hulda