Ministar ta bayyana cewa akwai matakai da ake bi domin biyan irin wadannan kudaden. / Hoto: Facebook/Oluwatoyin Sakirat Madein

Akanta Janar ta Nijeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kudi a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda take mayar da martani game da wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ma’aikatar ayyukan jinkai ta nemi a biya kudin tallafi ga wasu ‘yan kasar da ke cikin talauci.

A bayanin da ta yi, ta ce ana ware wa kowace hukuma kasonta a cikin kasafin kudi kuma kowace hukuma ita ke da hakkin aiwatar da wadannan ayyuka da kuma biyan kudin ayyukan.

Tun bayan da aka ga wata takarda dauke da sa hannun ministar ayyukan jinkai ta Nijeriya Betta Edu inda ta bayar da umarnin biyan kudin rage radadin talauci har sama da miliyan 500 a asusun bankin mutum guda ake ta ce-ce-ku-ce.

Dakta Oluwatoyin ta ce duk da cewa ofishinta ya samu bukatar biyan wadannan kudade daga ma’aikatar, amma bai biya ba. Ta bayyana cewa sai dai ta bayar da shawara ga ma’aikatar kan irin matakan da ya kamata ta dauka domin ganin an biya wadannan kudaden.

Akanta Janar din ta bayyana cewa irin wadannan lamura na biyan kudi sun shafi ma’aikatu ne, kuma babu wasu makudan kudade da za a iya biya ga asusun wani mutum daya da sunan Akanta mai gudanar da ayyuka.

A cewarta, ya kamata a tura wa wadanda za su yi amfani da tallafin kowa a asusun bankinsa.

TRT Afrika