Jumhuriyar Dimukradiyyar Congo, matattarar annobar farankamar biri, wato mpox ta ƙaddamar da babban gangamin rigakafi kan cutar a gabashin birnin Goma na ƙasar.
An bayar da rigakafin ta farko ga jami'an asibiti ranar Asabar, inda shirin zai mai da hankali kan gabaɗaya al'umma daga ranar Litinin a gabashin ƙasar, wurin da cutar ta fara ɓarkewa shekara guda baya.
Jami'ai sun gabatar da bikin fara rigakafin a wani asibiti da ke gabashin birnin Goma na ƙasar.
Ma'aikatar Lafiya ta ƙasar ta yi gargaɗi ranar Juma'a cewa faɗin shirin zai taƙaita sakamakon ƙarancin kayan aiki.
A yanzu, alluran ragakafi 265,000 ake da su, duk da ana sa ran zuwan wasu nan gaba.
Matsalar lafiya ta gaggawa
Fara rigakafin mataki ne da zai shawo kan rashin daidaito da ya bar ƙasashen Afirka da rashin alluran da aka yi amfani da su don yaƙar ɓarkewar cutar a 2022 a faɗin duniya, duk da ana samun allurar sosai a Turai da Amurka.
"Shirin yin rigakafin muhimmin mataki ne da zai daƙile yaɗuwar cutar da tabbatar da kare lafiyar iyalai da al'ummomi," cewar daraktan Afirka na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Matshidiso Moeti a wata sanarwa.
Farankamar biri tana yaɗuwa ta hanyar mu'amala ta kusa da mai cutar. Duk da ba ta faye muni ba, amma takan yi kisa a wasu lokuta kaɗan.
Takan haifar da alamomin cuta masu kama da mura da ƙuraje masu ɗurar ruwa a jiki.
A watan Agusta, WHO ta ayyana ɓarkewar annobar cutar mai barazana ga duniya, bayan gano wani nau'inta.
Congo DR ta ba da rahoton kamuwar mutane sama da 30,000 da aka tabbatar, da kuma mutuwar 990 tun a farkon 2024, wanda adadin shi ne kashi 90 cikin 100 na duka cutar da aka samu a Afirka zuwa yanzu a wannan shekara, cewar WHO.