An gano cutar Lassa a Nijeriya a karon farko a 1969 Photo/ AA

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Nijeriya NCDC ta ce mutum 142 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Lassa daga farkon 2023 zuwa yau.

Ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata.

NCDC ta ce an gano mutum 784 da suka kamu da cutar ta Lassa a jihohi 23 na kasar daga farkon Janairu zuwa yanzu.

A kididdigar da hukumar ta fitar, ta ce daga makon farko zuwa na 11 na bana, ana hasashen cewa mutum 3826 suna dauke da cutar, amma mutum 784 ne aka tabbatar da suna dauke da cutar sa’annan mutum 142 suka rasu.

NCDC ta bayyana cewa a jumlace, zuwa yanzu jihohi 23 a kasar kowace tana da akalla mutum daya da aka tabbatar ya kamu da cutar a kananan hukumomi 97.

Yadda za ku kare kanku daga kamuwa da cutar Lassa

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Amurka CDC ta bayyana cewa hanya ta farko ta kare kai daga kamuwa da wannan cuta ita ce mutum ya guje wa mu’amala da beraye, musamman ma a yankunan da ake samun wannan cutar.

CDC ta ce akwai bukatar a rinka saka abinci a cikin kwanuka wadanda beraye ba su iya fasawa haka kumata ce akwai bukatar a rinka barin gida cikin tsafta a kullum domin guje wa beraye.

Haka kuma hukumar ta ce masu cin beraye na cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta inda ta ce a guji cin duk wani nau’i na bera. Sa’annan hukumar ta ce malaman lafiya su ma akwai rawar da za su taka wurin kiyaye yaduwar wannan cuta musamman idan an kawo mara lafiya mai duka da cutar ta Lassa.

Ana son malaman lafiya su rinka saka kayan kariya da suka hada da takunkumi da safar hannu da rigar kariya ta musamman da tabarau.

Haka kuma hukumar ta CDC ta ce hanya mai muhimmanci ta rage yaduwar wannan cuta ita ce wayar da kan jama’a musamman kan yadda za su rage yawan berayen da ke muhallansu.

Cututtuka masu yaduwa dai na daga cikin lamuran da ke haddasa mace-mace a Nijeriya.

Ko a makon nan sai da hukumar ta NCDC ta fitar da wata kididdiga inda ta nuna cewa daga 30 ga watan Janairun bana zuwa 05 ga watan Maris akalla mutum 52 cutar kashe a jihohi 21 na kasar.

TRT Afrika da abokan hulda