A kowacce shekara ruwa na cinye mutane 372,000. Hoto: Getty Images

Daga Paula Odek

A lokacin da ake jimamin Ranar Magance Halakar Nitsewa a Ruwa ta Duniya, ruwa ya cinye mai dafa abinci ga tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama.

Tafari Campbell, mai shekaru 45, na daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon halaka a ruwa, matsalar da kwararru suka bayyana a matsayin wata boyayyiya.

Irin wannan mutuwa na barin iyalai da abokan arziki cikin alhini. A yayin da suke jimamin rasuwar mai dafa musu abinci, Barack da Michelle Obama, sun bayyana cewa Campbell ya zama daya daga cikin iyalan gidan.

“A lokacin da muka fara haduwa da shi, kwararren mai dafa abinci ne a Fadar White House – kwararre kuma mai son dafa abinci,” in ji ma’auratan.

Sun kara da cewa “A shekarun baya-bayan nan, mun fahimci yadda ya kasance mutum mai nutsuwa, mai raha, mai matukar kirki da ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu.”

Ana dilmiyewa a ruwa ne a lokacin da kofofin numfashi na hanci da baki suka cika da ruwa, abin da ke hana mutum yin numfashi.

Idan mutum bai iya tasowa sama tare da shakar iska ba, sai jikinsa ya fara shakar iskar carbon dioxide tare da rasa oxygen, sai hakan ya fara barazana ga rayuwar mutum, in ji masana.

Yara kanana ne suka fi dilmiye wa a ruwa. Hoto: Getty Images

Mafi yawa yara kanana ne suka fi dilmiyewa a ruwa, kuma ‘yan tsakanin shekara daya zuwa 9 ne suka fi dilmiyewar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce sama da rabin wadanda ke mutuwa sakamakon dilmiyewa a ruwa na da shekaru 25 zuwa kasa.

Dilmiyewa a ruwa ne hanya ta shida da ta fi kashe masu shekaru biyar zuwa 14 a duniya. Mawakin Nijeriya Davido ya rasa dansa mai shekara uku sakamakon dilmiye wa a ruwa a watan Nuwamban 2022.

Iyalai da dama da ba su da galihu a duniya sun rasa masoyansu da yawa ba tare da sun samu wata kulawa ta kasa ko na kasa da kasa ba.

Na gaba-gaba wajen kisa

Sama da kaso 90 na wannan ibtila’i na afku wa a kasashe marasa galihu. Matasa da yawa na yin kacibus da ruwa inda ake rasa su ba zato ba tsammani, wanda hakan ke barin ‘yan uwa da abokan arziki cikin jimami.

Amma kuma, idan aka dauki kwararan matakan magance dilimiye wa a ruwa, za a iya samun sauki wajen rage yawan afkuwar wannan ibtila’i.

Malaman koyar da ninkaya da kwararru, kamar su Sara Kariuki, sun fitar da shirin wayar da kan jama’a game da kiyaye afkuwar dimiye wa a ruwa.

Sarah Kariuki, mai bayar da horon ninkaya ta ce ninkya motsa jiki ne mai amfani.

Shawarwarin Kariuki na da saukin bi, amma kuma suna da muhimmanci: “Babu wani, komai kwarewar sa wajen iya ninkaya, da kawai zai tunkari ruwa shi kadai.

Za a iya samun hatsari ba zato ba tsammani, kuma ba tare da tallafi ba, kuskure dan karami na iya janyo rasa rai.” Amma ta kara da cewa “Iya ninkaya abu ne da ke kubutar da rayuwa.”

Kare kai daga dilmiye wa a ruwa

Sanin abun da mutum ke yi na da matukar muhimmanci ga manya a lokacin da suke kusantar ruwa. Ninkaya bayan an sha barasa ko kwayoyi na iya sauya labarin inda haka kan iya janyo rasa rai.

Haka zalika, wasanni a kusa da wuraren ninkaya, kamar gudu, abu ne da ya kamata a nisanta don kar a zame a fada ruwa da zai iya janyo wa a dimiye.

Sanya idanun iyaye a ko yaushe na da matukar muhimmanci sosai don hana yara kanana dilmiye wa a ruwa.

Kariuki ya jaddada cewa ya zama lallai iyaye a ko yaushe su dinga bin yaransu a lokacin da za su je wanka a ruwa, sannan su kasance a kusa da su.

Ta kara da cewa ko da ruwa ba shi da zurfi to yana da hatsari ga yara kanana, kuma rashin sanya idanu a kan lokaci na iya janyo mummunan abu.

Domin rake hstarin dilmiyewa, ana iya samar da katanga, wadda za ta raba inda wajen ninkaya yake da cikin gida.

Sannan ana shawartar iyaye da su guji sanya wa yara tufafin ninkaya shudi, saboda kalar na yawan sajewa da cikin wajen ninkayar, gara a dinga saka musu wata kalar mai haske yadda za a iya ganin su sosai.

Matakan ceto

Rigunan hana nutsewa, musamman ga wadanda ba su iya ninkaya ba, abu ne da ya zama dole.

Kwararru sun ce idan kuna cikin hatsari a ruwa kar ku firgita. Hoto: Getty Images

Kariuki ta bayar da shawarar cewa “Idan ka ji za ka dilmiye a ruwa kar ka firgita, ka yi kokarin ninkaya da baya tare da yin kira da a zo a taimaka maka.”

Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa za ka iya taimaka wa wanda ke dilmiyewa ko da kana wajen ruwan ne.

A wata makala, kungiyar ta zayyana wasu dabaru kamar haka:

Kwararru na bayyana cewa ceto a kan lokaci da amayo da ruwan cikin wanda ya kusa dilmiyewan a da muhimmanci wajen ceton rai. Hakan na da kyau sosai musamman idan mai aikin ceto wanda ya samu horo ne.

Tabbatar da aiki da dokoki

Kwararru na cewa akwai bukatar a bayar da fifiko wajen bayar da ilimi ga dukkan mutane don su iya ninkaya da kuma koyon yadda za su bayar da agajin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.

Kokarin magance dilmiye wa a ruwa na bukatar hadin kai. Hoto: Getty Images

Kokarin magance dilmiyewa a ruwa na bukatar hadin kai daga daidikun mutane da al’umma baki daya da gwamnatoci.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa karfafa dokoki da tabbatar da aiki da su, sannan a dinga bayyana a ina ruwa yake, zurfinsa da kuma saka katanga a tsakaninsa da wajen da mutane suke giftawa.

Wadannan matakai na iya taimaka wa sosai wajen rage dilmiyewa a ruwa.

Samar da wuraren ninkaya masu sauki musamman a kauyuka, inda aka fi yawan samun dilmiye wa a ruwa.

Kwararru sun bayyana ruwa na magani, kuma ninkaya motsa jiki ne da yake sanya dukkan gabban mutum su motsa sosai.

Idan aka dauki matakan kariya, mutane a ko ina za su ji dadin ninkaya don nishadi da motsa jiki.

Wannan na da muhimmanci wajen magance yawaitar dilmiyewa saboda hatsarin jiragen ruwa.

TRT Afrika