Mutane sun mutu sakamakon ruftawar Masallacin Fadar Sarkin Zazzau

Mutane sun mutu sakamakon ruftawar Masallacin Fadar Sarkin Zazzau

Masallacin na da shekaru sama da 100 kuma kuma rufinsa na ginin kasa ne.
Masallacin na da shekaru sama da 100 kuma kuma rufinsa na ginin kasa ne. Hoto: NTA

Hukumomi sun ce akalla mutum takwas ne suka mutu sakamakon ruftawar Masallacin Fadar Sarkin Zazzau da ke jihar Kaduna ta Nijeriya.

Kazalika mutum 21 ne suka jikkata sanadin iftila'in wanda ya auku yayin da ake gabatar da Sallar La'asar a ranar Juma'ar nan.

Kakakin Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan an yi jana'izar mutanen da suka rasu.

Da ma dai ganau sun shaida wa TRT Afrika cewa kusan mutum 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon ruftawar masallacin wanda aka gina fiye da shekaru dari da suka gabata.

Ganau sun bayyana cewa an dauki wadanda suka jikkata a motar mai martaba sarkin Zazzau zuwa asibitin Wusasa, daga bisani kuma jami'an kwana-kwana da na hukumar kiyaye hadurra sun je wajen don kai agajin gaggawa.

Wani mutum da ya ga lokacin da ginin ya rufta Abubakar Nabango ya shaida wa TRT Afrika cewa ana cikin yin Sallar La'asar ne sai wani bangare da ke tsakiyar masallacin ya rufto ya fada kan masu yin sallah a wannan lokaci.

"Wajen ya turnuke da kura ta yadda su kansu masu ba da agajin gaggawa ba su iya shiga ba sai da suka yayyafa ruwa saboda su samu damar kai wa jama'a dauki.

"Tuni kuma aka kai wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban da ke fadin garin Zariya, sannan hukumomin ba da agaji da dama sun je wajen ba tare da bata lokaci ba," in ji shi.

Shi ma wani ganau Bashir Abbakar Magaji da yake cikin masallatan, ya gaya wa TRT Afrika cewa "muna cikin sallah sai muka ji liman ya katse yana cewa 'don Allah jama'a a kawo dauki.'

"Nan da nan aka yanke sallah muka kutsa yankin inda muka iske wajen sahu biyu ne ginin ya rufta a kansu, kuma da mu aka dinga kwashe kasa da kokarin tono wadanda kasar ta rufe

Mutane sun ce yanayin damina da ake ciki ne ya jawo wannan iftila'i saboda akwai inda ruwa ke shiga ta saman rufin, "sai dai ba a mayar da hankali a kan hakan ba," a cewar Nabango.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya gaya wa TRT Afrika cewa "dama tun kwanakin baya akwai wadanda suka lura akwai inda ya fara tsagewa sannan suka bukaci a yi gyara, amma ba ni da tabbas ko sun mika wa hukumar masarauta batun.

"To burbushin ginin da ya fara rushewar dama yau an lura ya fara zuba, ba dadewa kuwa sai ga shi ya rufta," ya ce.

Masallacin dai dadadde ne mai tsohon tarihi wanda a shekarun baya-bayan nan aka sabunta gininsa ba tare da lalata asalin ginin kasar da aka yi na aihini ba.

An yi amannar cewa wani tsohon magini na wancan zamanin Muhammadu Durugu da aka fi sani da Muhammadu Babban Gwani ne ya gina masallacin ginin kasa tun lokacin Sarki Abdulkarim, shekara fiye da 180 da suka wuce.

TRT Afrika