Shugaba Tinubu na daga cikin shugabannin duniya da suka halarci taron G20. Hoto/BAT

Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba wa takwaransa na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa don kare mulkin dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar.

Mista Biden ya bayyana haka ne ranar Asabar yayin ganawarsa da Mista Tinubu a gefen taron kungiyar kasashen G20 da ake yi a Delhi na kasar Indiya.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce Mista Biden ya “gode wa Tinubu bisa kwakkwaran jagorancinsa a matsayinsa na shugaban Economic Community of West African States wajen karewa da tabbatar da dimokuradiyya da doka a Nijar da ma yankin baki daya.”

A karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ne kungiyar ECOWAS ta matsa wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar lamba kan lallai su mika mulki ga Bazoum ko kuma ECOWAS din ta yi amfani da karfin soji.

Sai dai sojojin Nijar din sun ce za su mayar da martani kan duk wata barazana ko kuma hari da aka kai musu.

Haka kuma Shugaba Biden ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan matakan da yake dauka domon farfado da tattalin arzikin Nijeriya.

A ranar da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki ya cire tallafin man fetur, matakin da Tinubun ya ce zai habaka tattalin arzikin kasar da kuma hana kasar ciwo bashi wanda take amfani da shi wurin biyan talllafin fetur din.

Haka kuma gwamnatin Shugaba Tinubun ta karya farashin naira da yin wasu sauye-sauye a hada-hadar kudade da zummar habaka tattalin arzikin kasar, duk da cewa wasu masu sharhi na kalubalantar matakan.

Shugaba Biden din ya bayyana cewa gayyatar da aka yi wa Nijeriya zuwa taron G20, wata manuniya ce kan yadda kasar ke taka muhimmiyar rawa a matsayin kasar Afirka mafi girma ta fannin dimokuradiyya da tattalin arziki.

TRT Afrika