Wani mai gabatar da ƙara a Jamhuriyar Benin ya ce hukumomin ƙasar suna tsare da ‘yan ƙasar Jamhuriyar Nijar biyar bisa zargin shiga wurin da bututan man fetur suke a iyakar Seme-Kpodji – abin da ke ƙara fito da yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis mai gabatar da ƙara na musamman Mario Metonou ya ce mutanen sun shiga wurin da bututan man ne a asirce kuma ya yi zargin cewa mutum biyu cikinsu na yi wa gwamnatin sojin Nijar leƙen asiri ne. Ko da yake ya ce ana ci gaba da bincike kan ainihin dalilin da ya kawo su wurin.
Ministan Man Fetur na Nijar Mahamane Moustapha Barke Bako ya yi watsi da zargin da mai gabatar da ƙara ya yi, inda a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Yamai kuma ya ce mutanen da aka kama jami’ai ne da ke duba aikin loda mai kamar yadda aka yi yarjejeniya da Benin.
Dangantaka tsakanin ƙasashe biyu - waɗanda suke yankin Yammacin Afirka - ta yi tsami tun bayan da hukumomin Benin suka dakatar da wucewa da man Nijar ta cikin ƙasarsu a watan Mayu, inda suka buƙaci gwamnatin sojin ƙasar ta fara buɗe iyakarta da ita ta ƙasa da dawo da hulɗa da ita kafin ta yarda a ci gaba da wucewa da man.
A nasa ɓangaren, Ministan Shari’ar Nijar ya ce ƙasar za ta kai wannan batun gaban kotun warware harkokin kasuwanci da cinikayya a Afirka wato the Arbitration Court of the Organization for the Harmonization of Business Law in Africa.
Rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu ta samo asali ne bayan juyin mulkin watan Yulin shekarar 2023 wanda sojoji suka kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum – abin da ya jawo Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanya wa ƙasar jerin takunkumai har tsawon wata shida.
Bayan ɗage tukunkuman an yi zaton harkokin kasuwanci za su koma yadda aka saba a yankin Yammacin Afirka, sai dai Jamhuriyar Nijar ta ci gaba da rufe iyakarta da Jamhuriyar Benin.
Matakin da Benin ta ɗauka na hana fitar da man Nijar ta cikin ƙasarta ya kawo cikas ga shirin Nijar na fara fitar da man fetur zuwa ƙasashen duniya daga rijiyoyin mai na Agadem zuwa gaɓar tekun Benin, inda daga can za a riƙa loda man a cikin jiragen ruwa.