Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin kare rayukan 'yan Nijeriya sai da harin da aka kai a Jami'ar Tarayya ta Gusau ya jefa 'yan kasar cikin fargaba./Hoto: Fadar Shugaban Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin da gwamnan Jihar Zamfara ya yi cewa tana tattaunawa da ‘yan bindiga da ke addabar jihar.

Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris ne ya bayyana haka ranar Litinin a sanarwar da mataimakin darakta a ma’aikatarsa ya fitar.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da martani ne kan zargin da gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya yi cewa tana neman sulhu da ‘yan bindiga da suka kwashe shekara da shekaru suna kashewa tare da sace mutane a jiharsa.

“Ba tare da wata tantama ba, minista yana sanar da cewa babu wani jami’in gwamnatin tarayya da ke yin sulhu da dan bindiga ko kungiyar ‘yan bindiga. Sai dai gwamnati na ci gaba da tsayawa a matsayinta cewa tana neman duk wata hanya da za ta hana watsuwar zaman dar-dar da kuma dawo da zaman lafiya ga al’ummar da ‘yan bindiga suka addaba,” in ji sanarwar.

Hakan na faruwa ne kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun sace wasu daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, lamarin da ya jawo mummunar suka daga wurin ‘yan kasar, ko da yake an kubutar da wasu daga cikinsu kuma gwamnati ta ce tana yin bakin kokarinta domin ceto sauran.

Ministan ya bayyana takaicinsa game da yadda gwamnan jihar ya siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa “maimakon (gwamnan) ya yaba wa jami’an tsaro da gwamnatin tarayya bisa kubutar da daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusai, ya zabi ya siyasantar da al’amari mai sarkakiya domin cin ribar siyasa”.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda ke sace dalibai da mutanen gari suna neman kudin fansa. Sannan a lokuta da dama suna kashe wadanda suka sace.

TRT Afrika