Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya musanta wasu rahotanni da ke cewa yana sayar da guraben aiki ga jama’a.
A wata sanarwa da babban jami’in watsa labarai na kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Asabar, ya yi kira ga jama’ar Nijeriya musamman masu neman aiki su yi watsi da wannan raɗe-raɗin.
Kamar yadda Soneye ya bayyana, babu ƙamshin gaskiya a labaran da ake yaɗawa kan cewa kamfanin yana da guraben aiki na sayarwa ga duk mai son saye.
Ya bayyana masu yaɗa irin waɗannan a matsayin ‘yan damfara waɗanda ke son su cuci masu neman aiki.
Kamfanin na NNPCL ya kuma yi gargaɗi kan cewa a matsayinsa na kamfani mai yin takatsantsan, ɗaukar aiki a kamfanin lamari ne da ake yin sa kai tsaye ba tare da buƙatar sayar da wani gurbi ba.
NNPC ɗin ya ce duk wanda ya biya kuɗi domin samun aiki a kamfanin ya yi hakan ne bisa raɗin kansa.
A kwanakin baya ne dai kamfanin na NNPCL ya sanar da cewa zai ɗauki aiki.
Sai dai kwana ɗaya da sanarwar, sai shafin da ake rajistar ɗaukar aikin ya samu matsala na wani ɗan lokaci sakamakon miliyoyin mutanen da suke ƙoƙarin neman aikin na NNPC.
Jama'a da dama na kwaɗayin aiki a kamfanin mai na NNPCL saboda albashi mai tsoka.