Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) na kan gudanar da bincike kan wasu Amurkawa uku waɗanda ake zarginsu da hannu a yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a ranar Lahadin da ta gabata a Kinshasa, babban birnin ƙasar.
Waɗanda ake zargi da kitsa aika-aikar sun haɗa da wasu baƙi 'yan ƙasashen waje da 'yan Kongo, inda a halin yanzu ake tsare da aƙalla Amurkawa uku da wani ɗan Birtaniya daga cikin mutane 40 da aka kama bayan da sojoji suka samu galaba a kan maharan.
"A yayin da ake jiran sakamakon binciken da ake yi, gwamnati na son tabbatar wa jama'a cewa an ɗauki matakan ƙarfafa tsaro na cibiyoyi da jami'ai da na birnin Kinshasa," a cewar wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar.
Mutanen da suka kitsa yin juyin mulkin suna kai hari ne kan gidajen Firaministan ƙasar da kuma ministan tsaro da babban ɗan siyasa da ake kyautata zaton shi zai zama kakakin majalisa, a cewa rundunar sojin ƙasar.
Kazalika sun mamaye fadar shugaban ƙasa 'Palais de la Nation', wadda ke cikin wuraren da suka fi samun kariya a birnin.
Jami'an tsaron fadar shugaban ƙasar sun harbe ɗan siyasar Kongo mazaunin ƙasar Amurka Christian Malanga, wanda kuma shi ne jagorar yunƙurin juyin mulkin tare da wasu mutane uku.
Yunƙurin ban mamaki
Hukumomin ƙasar sun ce suna ci gaba da ƙoƙarin bankaɗo yadda ɗan Malanga mai shekaru 2, Marcel, wanda ya fita zuwa makarantar buga ƙwallon ƙafa a ƙasar waje kana ya dawo da yunkurin tsige shugaban ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka manya.
"Ɗana ba shi da laifi," a cewar mahaifiyarsa, Brittney Sawyer, a wata wasiƙar imel da ta aika wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.
Sawyer ta kasance tana yawan wallafa hotunan annashuwa na danginta a-kai-a-kai a shafukan intanet , cikin har da wani da ta wallafa a watan Disamba inda Marcel da wata 'yar'uwarsa da wani jariri suke rungume da juna cikin kayan Kirsimeti mai launi iri ɗaya.
A 2020, ta wallafa hotunan Marcel yayin da yake rawa a lokacin zaman kulle sakamakon ɓullar cutar Covid.
A wani saƙo da ta wallafa a shafin Facebook a ranar Litinin, cikin fushi Sawyer ta bayyana cewa ɗanta ya bi mahaifinsa. "Wannan yaro ne da bai san komai ba kana ya bi mahaifinsa, na gaji da duk bidiyon da ake sakawa a ko'ina ana aiko mani, Allah ya kare ku!"
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan intanet ya bayyana yadda ɗanta tare da wani Bature ƙosasshe da ba a tantance ko wane ne ba, jikinsu duk ƙura kuma sojojin Kongo suna kewaye da su, Marcel ya ɗaga hannayensa saman fuskarsa a tsorace.
Mutumin dai ba shi ba ne wanda Marcel yake yawan wallafa bidiyonsa a shafukansa na Facebook da TikTok riƙe bandir ɗin kuɗade da kuma magana kan mata ba.
Mahaifinsa, Malanga ya bayyana kansa a shafinsa intanet a matsayin ɗan gudun hijira da ya samu ci gaba bayan zuwansa Amurka tare da iyalansa a shekarun 1990.
Ya kuma bayyana cewa ya zama shugaban jam'iyyar adawa ta Kongo kana ya hadu da manyan jami'ai a Washington da Vatican. Ya kuma bayyana kansa a matsayin miji na gari mai sadaukarwa kuma uban yara takwas.
Bayanan kotu da hirarraki maban-banta sun bayyana shi a matsayin wani mutum na daban.
'Yanayin bakin zuciya'
A 2001, shekarar da ya cika 18, an yanke was Malanga hukuncin zaman gidan yari har na tsawon kwanaki 30 a jihar Utah bisa laifin kai hari da makami da kuma shari'ar gwaji na shekaru uku.
Kazalika a shekarar, an tuhume shi da laifin cin zarafi da kuma laifin tada zaune tsaye, sai dai ya ki amsa laifinsa, kana aka yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi masa.
A 2004, an tuhume shi da laifin cin zarafi da kuma barazanar yin amfani da makami mai hatsari, amma ya ki amsa laifinsa, sai aka yi watsi da tuhumar.
Tun daga shekarar 2004, bayanai sun yi nuni da cewa lokuta da dama an yi ta samun tuhume-tuhume kan rigiginmu da tallafawa yara, sai dai babu tabbas ko sun shafi Sawyer.
‘Yan uwan Malanga sun taru a ranar Litinin da yamma a gidan mahaifiyarsa Chantal Malanga da ke West Jordan don jimamin abin da ya faru.
Sydney, wani dan uwan Christian Malanga, ya shaida wa AP cewa dangin na cikin “yanayin bakin zuciya” da “juyayi” bayan sumun labarin mutuwarsa. Suna tattaunawa game da shirye-shiryen yiwuwar jana'izarsa a jihar Utah, in ji ta, ba tare da bayar da wani ƙarin bayani ba.
Malanga ya bayyana kansa a matsayin wanda ya kafa jam'iyyar 'United Congolese Party' wani yunkuri da hada 'yan gudun hijira kamarsa.
Ya kuma bayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin "Sabuwar kasar Zaire" da ta yi gudun hijira tare da fitar da wasu bayanai da ke dauke da tsare-tsare da suka hada da samar da damammaki na kasuwanci da sake fasalin ayyukan tsaro na Kongo.
Hotunan Facebook da na shafinsa intanet dinsa sun nuna yadda ya gana da manyan jiga-jigan siyasar Amurka a lokacin, ciki har da tsohon 'dan jam'iyyar Republican Rob Bishop da kuma 'dan majalisar New York Peter King.
Bishop ya shaidawa AP cewa ba zai iya tuna lokacin da aka gudanar da taron ba ko kuma lokacin da aka dauki hoton ba. An kasa samun King domin jin tsokacinsa kan batun.
Wani mai bincike kan al'amuran Afirka da ke zaman kansa Dino Mahtani, ya ce ya soma jin labarin Malanga ne a shekarar 2018 a lokacin yana majalisar Dinkin Duniya a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasar DRC.
Ya ce hukumomin Kongo sun nuna zargin cewa Malanga na da hannu cikin wani yunkuri na kashe shugaban kasar na lokacin Joseph Kabila.
A wata hira da aka yi da shi, Mahtani ya ce bai taba haduwa da Malanga kai tsaye ba amma yana ganin yadda Malanga ke nuna kwadayinsa na samun damar yin mulki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo DRC.
Sannan ya yi hasashen cewa an ci amana tare da murafurtar Malanga a harin da aka kai a ƙarshen mako, la'akari da yanayin da aka kai harin.
"Wani ne ya yi masa makarkashiya. akwai yiwuwar daga waje ne, sai dai idan aka yi a'akari da dangantakarsa ta baya da daya daga cikin kwamandojin Soji gwamnatin Tshiskedi, za a ga cewa akwai yiwuwar ana sane da makircin cikin gida wanda hakan ya ba su damar daukar mataki cikin gaggawa.'' in ji Mahtani.
An soma yunkurin yin juyin mulkin ne a gidan 'dan majalisar tarayya Vital Kamerhe da ke Kinshasa, kana 'dan takarar shugaban majalisar dokokin Kongo. Masu gadinsa sun kashe maharan, a cewar jami'ai.
Daukar lamarin kai-tsaye
A bangare guda, Malanga na daukar bidiyon abin da ke faruwa a fadar shugaban kasar kai-tsaye. inda aka gan shi da wasu mutane sanye da kakin sojoji suna yawo cikin dare.
Daga baya ne aka kashe shi bayan ya ki miƙa kansa, in ji hukumomin Kongo.
Sai dai jami'an DRC ba su ce komai ba kan yadda maharan suka samu shiga ciki.
"Yana da matukar wahala a ce mutane 20 zuwa 30 za su yi tunanin cewa ta hanyar kutsawa fadar shugaban kasa da misalin karfe 4 na safe zai ba su damar kwace mulkin kasar ta Kongo," in ji Mahtani.
An bayyana ba’amurke na biyu da ake zargin da hannu a cikin yunkurin da Benjamin Reuben Zalman-Polun, a cewar hotunan takardar fasfo din Amurka da kafafen yada labarai na DRC suka yada.
Ya kuma kammala karatunsa a Jami'ar Colorado kana ya karanta fannin kasuwanci a jami'ar Georgetown, a cewar bayanan da kotu ta tattaro.
Daga baya ne ya fara kasuwancin kayayyaki sannan ya yi aiki a matsayin direban mota tura sakonni, in ji bayanan.
Alaƙarsa da Malanga ta kasance ta hanyar wani kamfanin haƙar zinare ne da aka kafa a Mozambique a shekarar 2022, a cewar labarin da wata jaridar gwamnatin Mozambique, da kuma rahoton da Africa Intelligence Newsletter suka fitar.
A shekarar 2015 ne Zalman-Polun ya amsa laifin fataucin muggan ƙwayoyi a Amurka, inda ya amince cewa ya haɗa baki da abokinsa wajen jigilar sama da kilogiram 20 na tabar wiwi daga wani gida a tafkin Tahoe na jihar California, zuwa ga kwastomominsa da ke faɗin Amurka.
Masu gabatar da kara sun buƙaci a yi masa sassauci, suna masu yin la'akari da " haɗin-kan da ya basu sosai" a yayin binciken da suka gudanar.
Kan wannan batu dai lauyansa bai ce komai ba a sakon da aika masa na neman jin martaninsa.
Kana babu wasu bayanai da aka fitar kan Ba’amurken uku har yanzu.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Kinshasa ya ce yana sane da cewa "Akwai yiwuwar hannun 'yan Amurka a kitsa yunkurin juyin mulki na ranar Lahadin da ta gabata,'' tare da ƙari a sanarwar da ya fitar kan cewa Ofishin za hada kai da hukumomin ƙasar '' yayin da suke gudanar da bincike kan waɗannan munanan laifuka da aka aikata.''