Ƴan Namibiya suna ƙada ƙuri’unsu ranar Laraba domin zaɓen sabon shugaban ƙasa da kuma ƴan majalisu a wani zaɓen da ake ganin jam’iyyar SWAPO mai mulki da ke neman tsawaita mulkinta na shekara 34 za ta sha wuya.
SWAPO ta mulki ƙasar ta kudancin Afirka tun lokacin da ta jagorance ta zuwa samun ƴancin kai daga gwamanti wariyar launin fata ta Afirka ta kudu a shekarar 1990.
Ƴar takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Netumbo Nandi-Ndaitwah, za ta kasance mace ta farko da za ta shugabanci ƙasar idan ta yi nasara.
Masharhantan siyasa sun ce rashin aikin yi da rashin daidaito da zargin cin hanci da rashawa sun janyo rashin amincewa ga jam’iyya mai mulki a zuƙatan mutane, musamman a tsakanin matasa, amma ana ganin tsoffi da ke ƙauyuka waɗanda suka daɗe suna goyon bayan SWAPO za su iya taimaka mata kaiwa tudun-mun-tsira.
"Zaɓe ne da zai fi tayar da hankali tun bayan samun ƴancin kai," in ji Henning Melber, wani jami’i a cibiyar nazari kan Afirka ta The Nordic Africa Institute wanda kuma ya daɗe a jam'iyyar SWAPO, wanda ya ce a karon farko yana ganin yiwuwar jam’iyyar za ta iya shan kaye.
"Matakin taƙaicin yana da yawa matuƙa."
Hanyar samun nasara
Wani likitan haƙori da ya rikiɗa ya zama dan siyasa Panduleni Itula, wanda shi ya zo na biyu a zaɓen da aka yi a shekarar 2019, yana sahun gaba cikin ƴan takarar jam’iyyun adawa 14.
A halin yanzu dai Namibiya na ƙarƙashin jagorancin shugaban riƙon ƙwarya Nangolo Mbumba, wanda ya karɓi ragamar mulki a watan Fabrairu bayan tsohon Shugaban Ƙasa Hage Geingob ya mutu. Sai dai shi ba zai yi takara ba.
Kafin ya yi nasarar cin zaɓen shugaban ƙasa dole ɗan takara ya samu kashi 50 cikin 100 na ƙuri’un da aka ƙada, idan ba haka ba zaɓen zai shiga zagaye na biyu.
Ƴan Namibiya za su kuma zaɓi ƴan majalisu.
Kimanin mutum miliyan 1.4 ne aka yi wa rijista domin kada kuri’u a ƙasar da ke da ƙarancin jama’a inda jumullarsu bai wuce kimanin mutum miliyan uku ba, in ji hukumar zaɓe.
Ana tsammanin sakamakon zaɓe nan da ƴan kwanaki kaɗan.