#LFP36 : Coup in Niger / Photo: AFP

Biyo bayan juyin mulkin Nijar, Nijar ta zama wata kasa daga yankin Sahel da ake yada labaran karya a kanta yayin da kasashen Yammacin Afirka suke kokarin tunkarar warware rikicin siyasar kasar.

Daga jitar-jitar karya da bidiyo da kuma muryoyin karya, kafar yada labarai ta AFP ta bi diddigin wasu labarai da aka wallafa a kafafen sada zumunta da ke goyon baya ko kuma adawa da jagororin juyin mulki, bayan kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Jim kadan bayan hambarar da gwamnatin, an yada wani bidiyo a intanet da ke ikirarin nuna gangamin magoya bayan Bazoum a birnin Yammai a ranar 6 ga watan Agusta. Batun gaskiya an dauki bidiyon ne ranar da aka hanbarar da shugaban daga mulki.

Wani bidiyo da ya karade intanet ya yi ikirarin nuna ministan kudin hambararriyar gwamnati yana kuka, bayan da jagororin juyin mulkin suka ba shi wa'adi kan ya ba su bayani dalla-dalla game da wasu kudade da suka bace, ko kuma su kashe shi.

Amma binciken da AFP ta yi na nuna cewa an dauki bidiyon ne a shekarar 2021, kuma tsohon ministan shari'ar Nijar Marou Amadou ne, lokacin da yake godiya ga tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou.

Akwai wasu rahotanni marasa tushe dangane da tsoma bakin kasashen ketare a rikicin yayin da ake fargaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta za yi amfani da karfin soji.

Kungiyar ECOWAS wacce Shugaban Nijeriya Bola Tinubu yake jagoranta ya yi Allah-wadai cikin hanzari kan fikar da gwamnatin Bazoum kuma ta kakaba takunkumai a kan Nijar kwanaki kadan bayan juyin mulkin, inda Nijeriya — wadda Nijar ta dogara da ita sosai kan wutar lantarki — ta yanke wutarta.

An yi ta Allah wadai da juyin mulkin da sojojin suka yi a Nijar

Akwai kuma wasu labaran karya kan jiragen yakin Faransa da aka ce sun sauka a Senegal don mara wa dakarun ECOWAS baya, ko kuma labaran mayaka sojojin haya daga Rasha na kungiyar Wagner da kuma batun cewa dakarun Burkina Faso sun isa Nijar don taimaka wa jagororin juyin mulkin.

'Karuwar' ra'ayin kin jinin Kasashen Yamma

Nijar ta kasance kasa ce da ba ta da teku, ta shiga sahun makwabtanta wato Mali da kuma Burkina Faso na zama kasa ta uku a yankin Sahel da aka yi juyin mulki a shekara uku.

Kamar sauran wurare a yankin, ana ci gaba da samun karuwar kin jinin kasar Faransa a Nijar.

Jagororin juyin Nijar sun samu goyon baya daga Mali da Burkina Faso wadanda su ma Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka, wadanda suka karkata ga Rasha kuma suka juya wa Faransa baya a kokarin karfafa dangantakarsu da Rasha.

A watan Mayu, Bazoum ya shaida wa jaridar The Independent ta Birtaniya cewa sojojin Wagner suna "yada labaran karya game da mu."

Shugaba Tinubu na Nijeriya ya yi Allah wadai da juyin mulkin a matsayinsa na shugaban Ecowas

Wasu masu sharhi kan al'amura sun ce akwai wasu tsare-tsare na yada labaran karya kamar yadda aka gani a wasu kasashen Afirka.

Labaran karya da aka rika yada wa tun bayan juyin mulki a Nijar "ba su yi kama da wadanda aka zauna aka tsara sosai ba," in ji Ikemesit Effiong wani mai sharhi a cibiyar nazari ta SBM Intelligence da ke Nijeriya.

Ko da yake, masu goyon bayan juyin mulkin "suna yada barazanar yaki da ECOWAS musamman da Nijeriya da kuma Faransa, don tattara mutane a kasa da kuma a intanet" wannan na faruwa ne a yankin "da ake samun karuwar kin jinin mulkin mallaka da kin jinin Kasashen Yammacin Duniya kuma abin na ci gaba da samun karin karbuwa," in ji Effiong.

Gungun masu yada farfagandan kaunar Rasha

Masana sun shaida wa AFP cewa salon yadda ake yada labaran karya kan Nijar ya yi kama da wanda aka taba gani a wata kasa a nahiyar: galibi yana farawa ne da kafa sadarwa, mai tabbatar da sirrin masu amfani da ita, kamar Telegram da WhatsApp kafin a yada su a wasu kafafen sada zumunta.

Ko da yake shafukan da ke nuna kin jinin Faransa da wadanda suke nuna kaunar Rasha da ke yada farfagandan kan Mali da Burkina Faso duka sun yada labarin karya game da Nijar.

Wasu 'yan Nijar da dama sun nuna kaunar Rasha bayan da ta nuna goyon bayan mulkin soja. Hoto: AFP

Daya daga cikin masu yin haka shi ne Pan-African Group for Trade and Investment (GPCI), wata kafar yada labarai da wani dan kasuwa mai son kasar Rasha Harouna Douamba ya kafa, wanda dan asalin Burkina Faso ne.

Kafar yada labaran GPCI tana gaba-gaba a cikin shafukan intanet da ke yada labaran karya don tayar da tarzoma, kamar yadda wata kungiya mai nazari kan sojojin haya na Wagner (All Eyes on Wagner) ta bayyana.

Misali, AFP ya gano daya daga cikin shafukan intanet na GPCI ya yi zargin cewa Faransa tana shirin "dagula al'amura" a Faransa da kuma bai wa "'yan ta'adda makamai".

Har ila yau GPCI ya wallafa gargadi kan yin amfani da karfin soji "daga wani shafi da ke yada labaran karya" misali a Chadi da Nijeriya, kamar yadda wani Bafaranshe, mai sharhi wanda yake tafiyar da shafin Twitter na Casus Belli, wanda yake nazari kan labaran karya a Afirka.

Mai sharhin wanda ya yi magana da AFP, inda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce kafar yada labarai ta GPCI ta harshen Faransanci don Afirka tana yada labaran karya.

Kafar yada labaran da ke kasar Kamaru ta yi hadin gwiwa da kafar yada labarai mallakin gwamnatin Rasha wato Russia Today kuma tana yawan kawo rahotanni kan aikace-aikacen kungiyar Wagner a Afirka.

A ranar 8 ga watan Agusta, tashar ta wallafa wani bidiyo da ke ikirarin nuna Bazoum cikin kwanciyar hankali bayan wai ya sanya hannu kan takardar yin murabus dinsa.

Hanbararren shugaban ya kasance a tsare tun ranar 26 ga watan Yuli, inda Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da "mummunan yanayin da Shugaba Bazoum da iyalansa suke rayuwa wanda rahotanni suka bayyana."

Wadannan jerin labaran karyan aiki ne na wasu da ake amfani da su daga ketare, in ji Maixent Some, wani mai nazari kan harkokin kudi a Burkina Faso wanda kuma yake bibiyar labaran karya masu alaka da Afirka a kafafen sada zumunta.

"Da ma akwai kin jinin Faransa tin kafin zuwan Rasha" kuma sai Rasha take kokarin cin moriyar hakan, kamar yadda ya shaida wa AFP.

Ko da yake masu fafutika 'yan asalin Afirka suna amfani da huldarsu da Rasha wajen kara cimma "manufofin kansu", ciki har da burinsu na siyasa.

TRT Afrika