Hukumomin Kenya sun ce sun dage haramcin sare itatuwa na shekara 6 ne saboda samar da ayyukan yi. Hoto: AP

Daga Dayo Yusuf

Masu rajin kare muhalli na nuna damuwa kan matakin kasar Kenya na dage haramcin da ta sanya na sare manyan itatuwa shekaru 6 da suka wuce, suna masu cewa hakan zai kawo koma-baya kan ci-gaban da aka samu lokacin da aka hana sare su.

"Idan muka fara sare itatuwa a wannan kasa, nan da 15 za mu fuskanci matsala lokacin da bishiyoyin da aka shuka suka kamata su girma," kamar yadda mai fafutikar kare muhalli George Mwaniki ya shaida wa TRT Afrika.

"Ba mu kai adadin da ake bukata ba a alkinta dazukanmu saboda haka ya kamata ne mu karfafa gwiwar dasa bishiyoyi ba sare itatuwa ba," kamar yadda ya bayar da shawara.

Shirin "take-it-easy" ya ja ankalin mutane ne bayan da Shugaba William Ruto ya fara sanar da shi a coci cewa gwamnati ta dage haramcin sare itatuwa saboda samar da ayyukan yi a kasar wadanda ake bukatarsu fiye da kowane lokaci.

"Ba zai yiwu a ce muna da manya-manyan itatuwa suna rubewa a dazuka yayin da mutanenmu suke shan wahala saboda rashin bishiyar timba ba. Wannan shirme ne," in ji Shugaba Ruto.

"Wannan ne ya sa muka ga ya kamata mu bude dazuka kuma sare icen timbar – saboda mu samar da ayyukan yi ga matasanmu da fadada kasuwanci."

Mutane da yawa suna ganin matakin zai kawoi koma-baya ga shirin gwamnati na yaki da sare dazuka.

Masani kan sauyin yanayi John Kioli ya ce babbar damuwarsa ita ce yadda za a aiwatar da abin.

Ma'aikatan kula da dazukan Kenya yayin da suke gyara wata wayar da aka yi wa Dajin Eburru shinge da ita. Hoto: Reuters

"Wane ne zai rika sanya ido kan sare bishiyo yadda ya kamata? Yaya za mu iya tabbatar da cewa bishiyoyin da aka sare manya ne? Me ya sa muke bude duka kofofinmu?" in ji shi. "Zai fi kyau a ce an fara abin ne a wani bangare na kasa don ganin yadda zai gudana. Idan abin ya tafi yadda ake so, za ka iya bude dazuka a sauran sassan kasar."

Tsarin tafiyar da aikin

Hukumar da ke kula da dazuka a Kenya ta fito ta nuna goyon baya ga matakin da Shugaba Ruto ya dauka.

"An samar da tsarin samarwa da sanya ido da kuma yadda za a sare itatuwan," kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter. "A wani bangare na tsarin, an samar da wata takardar shaida ga manhajojin dazuka kafin a amince a sare kowace bishiya."

Hukumar ta ce za ta tsara lokacin da za a fara sare itatuwan da kuma lokacin da za a dakatar da hakan. "Bayan kammala sare itatuwan, za a samar da wata takardar da ke nuna cewa an bi dukkan ka'idodin da aka gindaya."

Kazalika ana sa ran gwamnati za ta samu haraji daga sare itatuwan.

Kamar yadda bangaren da ke kula da dazukan ya ce dage haramcin sare itatuwan daji ya biyo bayan wata kididdiga da tattara bayanai ne da aka yi.

Shugaban Kenya William Ruto ya kaddamar da shirin dasa bishiyoyi. Hoto: Kenya Forest Service

Mai kare muhalli Mwaniki yana kallon batun ta fuskar amfani da kuma illolinsa.

A bangare daya, Kenya tana son cimma bukatarta ta amfani da timba a cikin gida yayin da a daya gefen akwai barazanar lalacewar muhalli.

"Yawancin kasashe makwabtanmu ba su da manyan dazuka. Amma kuma mu muna kashe makudan kudi duk shekara wajen sayen timba," in ji shi.

"Idan ka kalli Afirka gaba dayanta, to zai fi kyau mu rika sare itatuwan timba daga dazukanmu maimakon sayo su daga waje, kuma hakan zai sa mu daina kashe kudi da yawa. Amma gaba daya ba mataki ba ne mai kyau idan ka kalle shi ta fuskar alkinta dazuka."

Wani masanin muhalli Dokta John Recha ya ce wannan mataki na da matsaloli da dama.

A cewarsa dole sai duka hukumomi da masu ruwa da tsaki sun yi aiki tare da kaucewa matsalolin da ka je su zo.

"Kalubalen dage haramcin ba tare da shigo da manyan hukumomi masu ruwa da tsaki ba kamar Hukumar da ke Kula da Dazuka a Kenya shi ne wasu 'yan kasuwa za su iya cin karensu ba babbaka," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Wani babban abin nazari kan Kenya

Wani nazari na Huumar Majalisar Dinkin da ke kula da harkokin muhalli (UNEP) ya nuna cewa makudan kudin da ake kashe wajen sare itatuwa ya fi kudin da za a samu na riba bayan sayar da itatuwan da kaso 4 cikin 1.

Dokta Recha ya bayyana wuraren da za a iya samun matsala.

"Ci gaba da sare itatuwa zai haddasa karuwar zafin yanayi da kwararowar hadama da kuma wasu matsaloli ga al'ummar da ke zaune a kusa da dazukan."

Duka masanan sun fito da hujjoji kan a yi ko kada a ci gaba da sare itatuwan.

Yayin da Kenya ta zabi amfanin da za ta samu ta fuskar tattalin arziki ta hanyar yarda a sare manyan itatuwa bayan shekara shida da sanya haramcin yin haka, mutanen da suka damu da makomar duniya za su ci gaba da kiraye-kiraye sanya haramci kan sare itatuwa.

Amma wadanda suka yi nasara tsakanin bangarorin biyu za su so a sanya ido kan sare-saren itatuwan, ko ma dai mene ne da wuya bishiyoyin su tsira daga sarewa.

TRT Afrika