Ana gudanar da zanga-zangar ne a faɗin jihohin Nijeriya. / Hoto: Reuters

Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta soma gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.

Ana gudanar da zanga-zangar ce duk da yunƙurin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi na dakatar da ita.

Haka kuma zanga-zangar ta biyo bayan wa’adin mako biyu da ƙungiyar ƙwadagon ta bai wa gwamnatin tarayyar ƙasar domin ta samar da matakai waɗanda za su rage tsadar rayuwa a ƙasar.

Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar.

A Jihar Legas, masu zanga-zangar sun taru a Ikeja ƙarƙashin gada kuma rahotanni sun ce ɗimbin jama’a ne suka taru.

A Jihar Oyo kuwa, mambobin na NLC sun taru a sakateriyar ƙungiyar da ke Agodi a Ibadan babban birnin jihar.

A Kaduna ma haka abin yake inda mambobin ƙungiyar suka taru a sakateriyar ƙungiyar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fito tun kimanin bakwai na safe. / Hoto: Reuters

Raba ruwa da biskit

Tun kafin soma wannan zanga-zanga, ƴan sandan Nijeriya sun ta jan kunnen masu niyyar fita zanga-zangar kan tayar da tarzoma.

Sai dai a Jihar Legas, wani bidiyo da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ƴan sanda suke raba ruwa da biskit ga masu zanga-zangar.

A cikin bidiyon, an ga yadda motar ƴan sandan ke ɗauke da robobi na ruwa da biskit inda ake bin motar a baya ƴan sandan na miƙa ruwan da biskit.

TRT Afrika