Ana gudanar da zaɓen ‘yan majalisa a ranar Lahadi a Senegal, inda sabbin shugabannin ke fatan samun rinjaye a majalisa domin ganin sun cika alƙawuran da suka ɗauka waɗanda suka sa aka zaɓe su a watanni takwas da suka gabata.
Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya samu nasara a cikin watan Maris inda ya yi alkawarin kawo sauyi a fannin tattalin arziki, adalci da kuma yaki da cin hanci da rashawa – inda ya bayar da ƙwarin gwiwa a tsakanin al'umma waɗanda galibi matasa ne inda suke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi.
Faye ya naɗa ubangidansa Ousmane Sonko a matsayin firaminista, bayan an hana shi neman tsayawa takarar shugaban kasa bayan shafe shekaru uku yana takun saka tsakaninsa da gwamnatin da ta gabata.
Faye da Sonko sun yi alƙawarin tafiyar da gwamnati a kan kishin Afirka a tsarin sassaucin ra’ayi inda suka lashi takobin ƙara haɓaka tattalin arziƙi tare da sake waiwayar kwantiragin man fetur da kamun kifi da kuma ƙara tabbatar da ikon ƙasar Senegal wanda suka yi iƙirarin an sayar da shi ga ƙasashen waje.
Sai dai majalisar dokokin da 'yan adawa ke jagoranta ta kawo cikas a watannin farko da gwamnatin ta yi kan karagar mulki, lamarin da ya sa Faye ya rusa majalisar a watan Satumba tare da kiran zaben gaggawa da zarar kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar yin hakan.
Za a soma jefa ƙuria a rumfunan zabe a kasar da ke yammacin Afirka da karfe 8:00 na safe (0800 agogon GMT), inda kusan masu kada kuri'a miliyan 7.3 za su zabi 'yan majalisa 165 na tsawon shekaru biyar.
Ƙasar Senegal ta yi nisa a mulkin dimokuradiyya yayin da wasu takwarorinta da ke yammacin Afirka ke fama da juyin mulki.