Za a buɗe taron na AU a ranar Asabar 15 ga Fabrairu. / Hoto: Reuters

Ana sa ran batun rikicin da ke ƙara ƙamari a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo zai zama ɗaya daga cikin abubuwa da za a mayar da hanakli a kai a yayin taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da za a buɗe ranar Asabar, inda shugaban kasar DRC ba zai halarci taron ba bayan da dakarun da ke samun goyon bayan Rwanda sun kwace wani babban birni na biyu a yankinsa.

Kungiyar ta kasashe 55 za ta gana a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, a daidai lokacin da nahiyar Afirka ke fuskantar munanan tashe-tashen hankula a DRC da Sudan, da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na rage taimakon da Amurka ke bayarwa, lamarin da ya shafi nahiyar matuƙa.

Shugabannin Afirka suna wakiltar kusan mutum biliyan 1.5 a cikin ƙungiyar da aka daɗe ana sukarta da nuna kasala da rashin kataɓus a abubuwa da dama da suka shafi nahiyar.

A yayin da ake kallon rikicin yankin gabashin DRC, kuma kungiyoyin kasa da kasa na ƙara nuna hatsarin da ake fuskanta, an soki kungiyar ta AU kan yadda take nuna rashin kataɓus, kuma masu sharhi sun bukaci a dauki kwakkwaran mataki game da hakan.

A ranar 8 ga watan Fabrairu ne shugabannin kasashen gabashi da kudancin Afirka suka yi kira da a tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba cikin kwanaki biyar, amma wani sabon fada ya barke a ranar Talata.

Shugaban AU mai barin gado Moussa Faki Mahamat ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a jiya Juma'a cewa "dole ne a kiyaye tsagaita bude wuta", inda ya kara da cewa akwai "babban taro" tsakanin kasashen Afirka don dakatar da fadan.

AFP