Al’ummar kasashen Njeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Ghana sun gudanar da Sallar Idi ranar Juma’a.
Sun yi sallar ce bayan an ga watan Shawwal ranar Alhamis a yankuna daban-daban na kasashen.
Hakan na nufin an kammala azumin watan Ramadan wanda aka kwashe kwana 29 ana yi a galibin kasashen.
Musulmai sun sanya sabbin tufafi suka fita filayen Idi don yin sallah.
A sakonnin shugabannin kasashen na karamar Sallah, sun yi kira da mabiya addinin Musulunci su yi aiki da darussan da azumin watan Ramadan yake koyarwa.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya yi kira ga al’ummar Musulmi ta yi aiki tukuru wajen kaunar juna da wanzar da zaman lafiya.

Sanarwar da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar ta ambato shi yana cewa yayin da Musulmai ke neman lada daga Allah kan azumin da suka yi, Shugaba Buhari ya bukaci kada “mu manta da muhimmancin darussan watan Ramadan wadanda suka hada da inganta dangantakarmu da na kasa da mu”.
Shi ma Shugaba Mohamed Bazoum ya yi wa Musulmai fatan alheri sannan ya yi addu’a ga sojojin kasar da ke fagen daga don tsare “kasarmu”.