Kasar Kongo na fama da rikice-rikice tsawon shekaru, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu. / Hoto: Reuters

An bude rumfunan zabe a ranar Laraba da safe a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo inda za a gudanar da babban zaben kasar wanda shugaba mai ci Felix Tshisekedi ke fafatawa da ‘yan adawa domin neman wani wa’adi a kasar da ke fama da rikici.

An bude rumfunan zaben da misalin 6:00 na safe agogon kasar, wato karfe 4:00 na asubahi agogon GMT. Ana sa ran kammala zaben da misalin karfe 5:00 agogon kasar.

‘Yan jarida daga kamfanin dillancin labarai na AFP sun ga mutum na farko da ya kada kuri’arsa a wata rumfar zabe da ke gabashin Kisangani, wanda yanki ne da ke awa daya gaba da sauran yankunan kasar.

Wadanda suka hau layin kada kuri’a kafin karfe 5:00 na yamma za a ba su lamba kuma rumfunan zaben za su kasance a bude har zuwa lokacin da za su dangwala, kamar yadda wani jami’in hukumar zaben kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Rufe iyakokin kasa

Gwamnatin kasar ta bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu, kuma kamar yadda aka gudanar da zabukan baya, gwamnatin kasar ta rufe iyakokin kasar da kuma dakatar da tashi da saukar jiragen sama.

Kusan ‘yan Kongo miliyan 44 ne za su jefa kuri’a, a kasar mai mutum miliyan 100, inda ake sa ran za su zabi shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da kuma na jihohi da kansiloli.

A karon farko, ‘yan kasar Kongo da ke zaune a Afirka ta Kudu da Belgium da Amurka da Faransa su ma za su kada kuri’arsu. Sama da mutum 100,000 suke takara inda suke neman kujeru daban-daban.

Duk da cewa za a soma kirga kuri’u da zarar an kammala jefa su, amma ba za a sanar da sakamakon zabe ba sai bayan an shafe kwanaki.

AFP