Yakin Sudan da ya barke a tsakiyar watan Afrilun 2023 ya yi sanadiyyar mutuwar dubunnan mutane. / Hoto: TRT Afrika

Mayakan RSF, da ke yakar sojojin Sudan sama da shekara guda, sun bude wuta tare da satar kayan kula da lafiya a yankin Darfur na yammacin kasar, inda suka tilasta aka rufe asibitin, in ji wata kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa.

RSF ta kai hari kan Asibitin Kudu na al-Fasher, babban birnin lardin Arewacin Darfur a ranar Lahadi, inda suka bude wuta kan ma'aikatan lafiya da marasa lafiya, in ji wata sanarwa da Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ta fitar.

Wannan na zuwa ne a yayin da RSF suka tsaurara hare-hare don ƙwace iko da garin, wanda nan ne waje na karshe mafi girma da ke hannun sojojin Sudan a yankin Darfur.

A makonni biyu da aka dauka ana fafata rikici a watan da ya gabata a ciki da kewayen al-Fasher, an kashe sama da mutum 120.

'Mummunan yanayi'

A yayinda ake ci gaba da gwabza yakin, rundunar soji ta hada kai da kungiyoyin 'yan tawaye inda suka kafa dakarun hadin gwiwa don rike iko da garin, inda dubunnan daruruwan wadanda aka raba da matsugunansu suka fake tun bayan fara rikicin.

"Abu ne mummuna a ce RSF sun bud ewuta a asibiti. Wannan ba lamari ne kebantacce ba, inda ma'aikata da marasa lafiya suke ta fuskantar hare-hare tsawon makonni daga dukkan bangarorin biyu, amma bude wuta a cikin asibitin ya keta iyaka," in ji Michel lacharite, shugaban sashen ayyuka na Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka.

A lokacin da aka kai harin, akwai marasa lafiya 10 da wasu ma'aikatan lafiya, inda ma'aikatan ceto da jami'an ma'akatar lafiya suka fara kwashe marasa lafiya.

Mafi yawan marasa lafiyar da ma'aikatan asibitin, ciki har da ma'aikatan Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka sun samu damar tserewa harbe-harben.

An harba ƙugiya zuwa asibitin

Ba a gama tabbatar da ko an samu asarar rayuka ko jikkata ba sakamakon harin, kamar yadda kungiyar bayar da agajin ta bayyana.

Kakakin RSF bai kira waya ba bayan da aka kira shi ba a same shi ba don ya ce wani abu game da batun.

A tsakanin 25 ga Mayu da 3 ga Yini, sau uku ana kai hari da bindigu d akugiya kan asibitin, inda aka kashe mutane biyu tare a jikkata wasu 14, in ji Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka.

A watan Afrilun bara aka fara rikicin Sudan a lokacin da rikici ya yi tsamari tsakanin shugabannin soji da na RSF, inda aka fara fafata rikici a Khartoum babban birnin kasar da ma wasu yankunan.

Yunwa

Yakin ya lalata Sudan, ya yi ajalin sama da mutane 14,000 tare da jikkata wasu dubunnai, inda kasra ta fada cikin yunwa.

Hukumar zamar da abinci ta MDD ta yi gargadi ga bangarorin da ke rikici da juna a watan da ya gabata cewa za a samu babban rikici na yunwa da rasa rayuka a Darfur da ma wasu yankunan Sudan, matukar ba su bayar da dama an kai wa mutane kayan agaji ba.

An bayyana samun cin zarafin mata da sauran ayyuka assha daga dukkan bangarorin, wanda dukkan su laifukan yaki ne, kamar yadda MDD ta bayyana.

TRT Afrika