Hukumar da ke nazari kan yanayin kasa ta Ghana ta bayyana cewa motsin kasar da aka yi kasar ranar Lahadi ba ta wuce maki 3.6 a ma’aunin Ritcher ba.
Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin wanda bai taka kara ya karya ba, tana mai bai wa mutane shawarar ci gaba da al’amuransu na yau da kullum.
“Motsin kasar kadan ne kuma ba a tunanin zai iya janyo wata matsala,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Ghana ya ambato sanarwar hukumar tana cewa.
Sanarwar da mukaddashin shugaban hukumar, Isaac Kuuwan Mwinbelle, ya sanya wa hannu ta ce lamarin ya auku ne kilomita bakwai daga Weije a tsakiyar Accra da misalign karfe 7:17 na safiya.
An ji motsin a Nyanyano Kakraba, Weija, Pokuase, Adenta, Kanda da kuma wasu sassan tsakiyar Accra.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan abubuwa tare da sanar da jama’a domin tabbatar da lafiyarsu.