An gudanar da jana'izar babban malamin addinin Musuluncin nan na Nijeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu, a Babban Masallacin Idi na garin Argungu da ke Jihar Kebbi a arewao maso yammacin Nijeriya.
Rahotanni sun ce dubban mutane da suka hada da manyan malamai da 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati ne suka halarci jana'izar malamin, wanda ya rasu ranar Laraba da marace.
Sheikh Giro ya rasu ne bayan fama da gajeriyar jinya, kamar yadda kungiyar Jibwis ta bayyana.
Cikin wadanda suka halarci jana'izar har da shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakataren Iala Sheikh Kabiru Haruna Gombe da Sheikh Dr Ibrahim Disina da Sheikh Jalo Jalingo da sauran manyan malamai na kasar.
Kazalika gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris da tsohon gwamnan SOkoto Aliyu Magatakarda Wamakko ma duk sun halarci jana'izar babban malamin.
Marigayi Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu, wanda ya rasu yana da shekara 71, shi ne Shugaban Kwamitin Ayukka Na Kungiyar Izala ta kasa.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu mutum ne da ba ya tsoron tsayawa don kare mutuncin talaka da kuma gaya wa shugabanni gaskiya.