Ana yawan samun rushewar gine-gine a Kamaru. Hoto/Reuters

Akalla mutum 12 sun rasu, sama da talatin kuma sun samu rauni bayan wani gini ya ruguje a birnin Douala na Kamaru.

Ginin mai hawa hudu ya rushe ne da safiyar Lahadi inda ya fada kan wani karamin gini, kamar yadda hukumomi suka shaida.

“Akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu. Masu aikin ceto da taimakon dakarun gwamnatin Kamaru na ci gaba da tono baraguzai domin gani ko za su samu karin mutane,” kamar yadda gwamnan yankin Littoral, Samuel Dieudonne Ivaha Diboua ya shaida wa manema labarai.

An bayar da umarni ga jami’an kashe gobara na sojojin kasar da su taimaka wa kungiyar Red Cross da sauran masu aikin ceto ci gaba da gano wadanda suka tsira da ke karkashin baraguzan.

Jama’a na cikin fargaba

Mazauna unguwar Ndogbon inda a nan ne lamarin ya faru sun ce sun kadu da abin da ya faru. “Mun ji mutane na ta ihu... inda muka yi kokarin taimaka wa wasu, amma muka kasa yin hakan da shebur da fatanyarmu,” in ji Gaspard Ndoppo wanda ke zaune a kusa da wurin da ginin ya rushe.

Ana yawan samun rushewar gine-gine a Douala, a wani lokacin saboda bala’i irin su zaftarewar kasa a wasu lokuta kuma rashin ingancin gine-gine, kamar yadda mazauna yankin da lamarin ya faru suka bayyana.

Gwamnatin Douala a halin yanzu tana rushe gine-ginen da aka yi a wuraren da ke cikin hatsarin ambaliyar ruwa ko kuma zaftarewar kasa.

Ginin da ya rushe a ranar Lahadi ba ya cikin gine-ginen da aka saka cikin jerin wadanda za a rushe.

AP