An yi girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.8 a Habasha, kamar yadda hukumomin da ke bincike kan ƙasa na Amurka da Jamus suka tabbatar a ranar Asabar.
Girgizar ƙasar ta fi tasiri a wani yanki mai nisan kilomita 142 daga Addis Ababa babban birnin ƙasar, kuma girgizar na da zurfin kilomita 10, in ji hukumar USGS ta Amurka.
Haka kuma wani dutse mai aman wuta da ke Tsibirin Dofen shi ma ya zubar da wuta bayan da aka shafe tsawon watanni ana samun ƙananan girgizar ƙasa kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Aden Bela wanda wani jami'i ne ya shaida wa kafar watsa labarai ta Habasha cewa dutsen ya dakatar da fitar da hayaƙi sai dai har yanzu akwai talgen wuta a ciki.
An kwashe mazauna yankin
Dubban fararen hula ne aka kwashe su daga yankin sakamakon fargabar da ake ciki na aman wutar dutse, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Juma'a.
Kwashe jama'ar na zuwa ne bayan an ga alamun hayaƙi na tashi daga wurin tun a ranar Alhamis, wanda hakan ya saka fargabar faruwar aman wutar
Hukumar a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta ɗauki matakin kwashe jama'ar ne domin yin taka-tsantsan. Ta bayyana cewa an kai mazauna wurin wani wuri mafi aminci a yankin.