Manufar kudurin shi ne hukunta yin zargin tsafi kan mutane, inda aka yi gyara kan tsohuwar dokar manyan laifuka ta 1960.
Burin dokar shi ne haramta ayyukan matsafa da masu kamen mayu, da masu ayyanawa ko jifan mutane da maita ko tsafi, da kuma batutuwa da suka jibinci haka.
Dan majalisa mai suna Mr. Francis-Xavier Kojo Sosu, mamba a jam'iyyar National Democratic Congress (NDC), wanda yake wakiltar mazabar Madina shi ne ya gabatar da kudurin gyaran dokar.
Sauran 'yan majalisar da suka goya wa kudurin baya sun hada da Hajia Laadi Ayii Ayamba, daga Pusiga, da Dr Godfred Seidu Jasaw, daga Wa East, da Madam Helen Adjoa Ntoso daga Krachi West, da kuma Madam Betty Nana Efua Krosbi Mensah, daga Afram Plains North.
Wani dan majalisa Mr Anyimadu-Antwi ya koka kan cewa "a duka fadin Afirka, Ghana ce kawai take da sansanin kamammun matsafa, wanda ya saba wa tsarin mulkin adalci, kasancewar ana gallaza musu azaba".
Dan majalisar ya kuma jaddada bukatar tallafi daga kungiyoyin sa-kai kamar su Action Aid, da Sanneh Institute, da Amnesty International, don kawar da haramtattun sansanonin kamammun mayu.