Aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu sakamakon wannan lamari. / Hoto: Reuters

An ji ƙarar harbe-harben bindiga a babban birnin Kongo da safiyar Lahadi inda wasu mutane ɗauke da bindiga sanye da kayan sojoji suka yi arangama da masu tsaron wani babban ɗan siyasar ƙasar a kusa da fadar shugaban ƙasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla mutum uku suka rasa rayukansu sakamakon rikicin, kamar yadda mai magana da yawun ɗan siyasar ya tabbatar wa kafafen watsa labarai na ƙasar.

Mutanen ɗauke da makamai sun far wa gidan Vital Kamerhe da ke Kinshasa, dan majalisar tarayya kuma tsohon mataimakin firaministan tattalin arziki, amma jami’an tsaronsa sun yi ba-ta-kashi da su, kamar yadda Michel Moto Muhima ya bayyana a shafinsa na X, wanda shi ne kakakinsa.

Kafofin yada labaran cikin gida sun bayyana mutanen a matsayin sojojin Congo.

Sai dai ba a bayyana ko suna kokarin kama dan siyasar ba, wanda dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Congo ne a zaben da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar din da ta gabata, amma aka samu jinkiri sakamakon takaddamar cikin gida ta jam'iyya mai mulki a ƙasar.

AP