Masu zanga-zangar sun kuma nuna kin amincewa da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar:Hoto/Reuters

Daruruwan mutane da ke goyon bayan juyin mulki sun taru a Yamai, babban birnin Nijar, wasunsu rike da tutar kasar Rasha, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Masu zanga-zangar sun taru ne a dandalin İndependence Square a tsakiyar birnin Yamai a ranar Alhamis, bayan kiraye-kirayen kungiyoyin fararen-hula don a fito a yi murnar zagayowar Ranar 'Yancin Kai daga kasar Faransa a shekarar 1960.

Wani mai zanga-zanga, Issiaka Hamadou, ya ce "tsaro ne kawai abin da ya dame mu," ba tare da la'akari da cewa ya fito ne daga hannun "Rasha ko China ko Turkiyya ba, idan har suna son su taimake mu."

"Mu dai ba ma kaunar Faransa, wacce ta rika yi mana sata tun shekarar 1960 – sun kasance tun lokacin kuma babu abin da ya canja," in ji shi.

Fargaba

Faransa tana da dakaru 1,500 a Nijar a wani yunkuri na yaki da masu tayar da baya a yankin Sahel.

"Ba ni da aikin yi bayan na yi karatu a wannan kasa, saboda gwamnatin (Bazoum), wacce take samun goyon bayan Faransa," in ji wani dalibi wanda ya ce sunansa Oumar. "Muna so duka wannan ya tafi."

Nijar ta fada rikici tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a makon jiya, abin da ya jawo musu kakkausar suka daga kasashe da kungyoyi.

Juyin mulkin ya sanya fargaba a kasashen Yammacin Duniya wadanda suke kokarin kawo karshen hare-haren masu tayar da kayar baya da suka ki ci suka ki cinyewa musamman a arewacin Mali tun shekarar 2012.

Yanzu rikicin ya yadu zuwa Nijar da Burkina Faso bayan shekara uku, kuma yana barazana ga kasashen da ke gabar Mashigin Tekun Guinea.

Masu goyon bayan gwamnatin sojin a Nijar sun ce Faransa ta kasa kare su daga kungiyoyin 'yan bindiga, yayin da Rasha take shirin zama babbar kawarsu.

TRT Afrika