Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun kubutar da 'yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan 'yan bindiga sun kashe 'yar'uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.
An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.
Sai dai daga bisani 'yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka bukaci ya nemo N60m a matsayin kudin fansa.
Lamarin ya dauki sabon salo bayan 'yan bindiga sun kashe Nabeeha a yayin da wata makusanciyarsu Asiya Adamu take tattara kudin fansar bayan ta roki mutane a shafukan sada zumunta.
Hakan ya sa 'yan Nijeriya suka rika kiraye-kiraye ga jami'an tsaro su yi gaggawar kubutar da ragowar 'yan mata.
Dajin Kajuru
Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta fitar ranar Asabar da tsakar dare, ta ce jami'ansu da na rundunar sojin Nijeriya sun kubutar da ‘yan matan 'yan'uwan Nabeeha.
Sanarwar ta ce an gano su ne a kusa da dajin Kajuru da ke Kaduna ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na dare.
Ta kara da cewa tuni aka kai 'yan matan gidansu da ke yankin Bwari a birnin na Abuja.