Akalla mutum 20 ne ake fargabar rushewar wani otel mai hawa hudu da ake ginawa a unguwar Life Camp da ke babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ya rutsa da su.
Gidan talabijin na kasar NTA ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Wasu da abin ya faru a gabansu sun ce fiye da mutum 20 ne ake zaton suna cikin ginin karkashin da yake wajen a yayin da ya rufta.
Ana yawan samun matsalar rushewar gini a Nijeriya, musamman a manyan birane irin su Abuja da Legas.
Ko a watan Fabrairun shekarar nan ma sai da wani rukunin shaguna da ake kan ginawa a unguwar Gwarinpa da ke Abuja ya rushe har ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da jikkata wasu.
Kawararu suna yawan cewa manyan matsalolin da ke jawo rushewar gini sun hada da amfani da kayan gini marasa inganci da rashin aiki mai kyau da rashin tuntubar kwararru a harkar gini da rashin bin ka'idojin gini da rashin saka tubali mai kyau, da sauran su.