Majalisar Dattawan Nijeriya ta sanar da sunayen manyan jagororin majalisar kasar.
Shugaban majalisar ta 10, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da sunayen a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Gidan talabijin na Nijeriya NTA ta ruwaito cewa Sanata Opeyemi Bamidele shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar.
Sannan tsohon gwamnan Ebonyi David Umahi shi ne Shugaban Marasa Rinjaye.
Sai kuma Sanata Ali Ndume Mai Tsawatarwa na masu rinjaye da kuma Lola Ashiru Mataimakin Mai Tsawatarwa na masu rinjaye.
Sannan kuma Simon Mwadkon shi ne Shugaban Marasa Rinjaye da kuma Oyewumi Olalere mataimakinsa.
Majalisar ta kuma sanar da Sanata Darlington Nwokocha a matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye da kuma Sanata Rufai Hanga mataimakinsa.
A ranar 13 ga watan Yuni ne aka rantsar da mambobin majalisar ta goma a zaurenta da ke Abuja.
Jagororin Majalisar Wakilan Nijeriya
Ita ma Majalisar Wakilan Nijeriya ba da jimawa ba ta sanar da jagororin majalisar inda kakakinta Tajudeen Abbas ya sanar da su.
A halin yanzu, Julius Ihonvbere shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar sai Usman Bello Kumo Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye da kuma Abdullahi Ibrahim Halims Mataimakin Shugaban Majalisa.
Sa’annan Adewumi Onanuga shi ne Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar, Kingsley Chinda shi ne Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar.
Ali Isa shi ne ya zama Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye sai Aliyu Sani Madaki Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye.
Haka kuma George Ozodinobi shi ne Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawan.