Aƙalla sojojin sa kai biyar aka kashe waɗanda ke aiki tare da sojojin Burkina Faso a wani hari da aka a ƙasar, kamar yadda hukumomin ƙasar suka sanar a ranar Asabar.
Hukumomin sun bayyana cewa 'yan ta'adda ne suka kashe sojojin sa kan a yankin Gnangdin wanda ke kusa da iyakar Togo da Ghana.
Akasari jami'in sa kan ana ɗaukar su aiki ne daga cikin jama'ar da ake bai wa tsaro sannan a ba su horo na wata uku kafin a ba su makamai.
A wani lokaci suna aiki tare da ƙwararrun sojoji wani lokaci kuma suna fita aiki da kansu.
Masu zanga-zanga sun rufe babbar hanya
Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a tsakanin mazauna yankin inda suka rufe babbar hanyar da ta hada yankin da kan iyakar kasar Togo, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP bisa sharadin sakaya sunansa.
Ya ce hanyar ta ci gaba da zama a rufe na tsawo sa'o'i kafin hukumomi suka zo suka buɗe ta.
"Akwai rundunar (sojoji) a yankin amma sai da suka ɗauki lokaci kafin su mayar da martani, wanda bai kamata hakan ya faru ba. Idan har ƙungiyoyi za su iya kai hare-hare duk da kasancewar waɗannan sojin, to akwai sauran aiki a gabanmu," in ji shi.
Rashin tsaro ya yi ƙamari a Mali a shekarar 2012 inda ya bazu zuwa Nijar da Burkina Faso.
Dukkan kasashen uku na yammacin Afirka gwamnatocin soja ne ke tafiyar da su.
Tun bayan ɓarkewar rikici a Burkina Faso a shekarar 2015, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 26,000 tare da tilasta wa aƙalla mutum miliyan biyu barin gidajensu, a cewar kungiyar sa ido ta ACLED.