Wani hari da aka ɗora alhakin kai shi kan ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qaeda ya yi sanadin mutuwar sojojin Mali aƙalla 15, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Mali ta shafe sama da shekara 10 tana fama da rikicin masu iƙirarin jihadi da na wasu ƙungiyoyin.
“Aƙalla sojojin Mali 15 aka kashe a ranar Alhamis a yayin wani harin kwanton-ɓauna da masu iƙirarin jihadi daga ƙungiyar Support of Islam and Muslims suka kai,” kamar yadda wani zaɓaɓɓen jami’in gwamnati daga yankin Mopti ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP inda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda yanayi na tsaro.
Majiyar ta ƙara da cewa akwai wasu “sojoji da suka ɓace da kuma jikkata.
Haka kuma akwai wani zaɓaɓɓen shugaba da ya tabbatar da wannan labarin inda ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai “sojoji 14 da jandarma ɗaya”.
“Akwai sojojin da suka ɓace, maharan sun kuma ƙwace kayayyakin yaƙi,” kamar yadda majiyar ta ƙara da cewa.
Haka kuma wani jami’i na daban ya shaida cewa an kai harin ne kilomita biyar daga ƙauyen Diallassagou inda ya ƙara da cewa “akwai sama da mutum 10 waɗanda suka ji rauni sannan sama da 15 suka rasu a sojojin Mali”.
Wani jami’in gwamnati na daban ya tabbatar da cewa an kai harin ne kilomita biyar daga ƙauyen Diallassagou inda ya ƙara da cewa “akwai sama da mutum 10 waɗanda suka jikkata sannan sama da sojojin Mali 15 suka rasu”.