Tun watan Afrilu Sudan ta fada rikici inda a kalla mutane miliyan biyar suka rasa matsugunansu. Hoto: Reuters.

Kazamin rikicin da aka fafata a yankin da Sudan da Sudan ta Kudu ke ikirarin mallakarsa ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 32, ciki har da sojin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, in ji mahukunta.

Fararen hular da sojin da ke aiki da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun mutu a yayin da 'yan bindigar da ba a san ko su waye ba suka kai hari kan kauyukan kudancin yankin Abyei, kamar yadda kafafan yada labarai na kasar suka rawaito.

Wata tashar rediyo da ke Sudan ta Kudu, Eye Radio Juba ta rawaito ministan watsa labarai na Abyei, Bolis Kuoch na cewa an kashe mutum 32, an jikkata wasu 20, "amma kuma an dakatar da artabun, lamarin ya kuma lafa."

Rikicin kabilanci da na kan iyaka ya tsananta tun bayan da Sudan ta Kudu ta jibge dakarunta a kan iyakarta da Sudan a watan Maris, in ji kamfanin dillancin labarai na AP.

Ofishin kula da dakarun wanzar da zaman lafiya da ke yankin ya soki jibge dakarun, yana mai cewa "hakan zai janyo wahalhalu da matsalolin jinƙai" ga fararen hula.

An aika da sojojin kasa da kasa zuwa ga gundumomin Aleel da Rum Ameer, a matsayin wani bangare na Ayyukan Samar da Tsaro na Wucin Gadi da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a yankin Abyei.

A makon da ya gabata, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kara wa'adin aikin UNIFSA har nan da 15 ga Nuwamban 2014.

A farkon wannan watan, Wakiliyar Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Kusurwar Afirka, Hanna Serwaa Tetteh ta yi gargadi da cewa rikicin sojojin Sudan da na mayakan RSF na kusantar Sudan ta Kudu da yankin Abyei.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe sama da mutane 9,000 tun bayan barkewar rikici a watan Afrilu, inda aka raba miliyoyi da matsugunansu a kasar ta Sudan, inda wausn su suka gudu kasashe makota.

Sudan da Sudan ta Kudu sun yi sabani kan waye ya mallaki yankin Abyei mai arzikin man fetur, tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga Sudan a 2005 bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta kawo karshen yakin basasar da aka yi tsakanin kudanci da arewacin Sudan.

Yarjejeniyar ta bukaci dukkan bangarorin da su warware matsayin karshe na yankin Abyei ta hanyar tattaunawa, amma hakan ba ta taba tabbatuwa ba.

TRT Afrika