Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tabbatar da kashe wasu gawurtattun kwamandojin ‘yan ta’adda uku a hare-hare ta sama da ta kai a cikin makon nan.
Daga cikin wadanda ta kashe akwai Machika da Haro da Dan Muhammadu da Alhaji Alheri wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje.
Daraktan watsa labarai na Hedikwatar Tsaron Nijeriya Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Asabar.
Buba ya bayyana cewa Machika babban dan ta’adda ne kuma ya gwanance wurin hada bama-bamai haka kuma ya kasance kane ga Dogo Gide. Sai kuma Haro da Dan Muhammadu sun kasance gawurtattu wurin garkuwa da mutane.
A sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa hari ta sama da kasa da dakarun suka kai a ranar 11 ga watan Disamba ne ya yi sanadin mutuwar Kachalla Kawaje, wanda shi ne babban jagora a wurin sace daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Zamfara.
Ya kara da cewa an kashe Kachalla a Karamar Hukumar Munya da ke jihar Neja a lokacin da yake tare da mayakansa a kafa.
Ya bayyana cewa harin da suka kai ya jawo ‘yan ta’adda 38 sun mutu sannan suka kama 159.
Ko a cikin watan nan sai da jirgin sojin Nijeriya ya halaka gomman 'yan ta'adda da baburansu 18 a cikin jirgin ruwa