An bai wa tawagar mai mutum huɗu, ƙarƙashin jagorancin shugabannin kamfanin Selcuk Bayraktar da Haluk Bayraktar lambar yabon ne a ranar Laraba Photo : Fadar shugaban kasar Mali

An karrama shugabannin kamfanin da ke ƙera jirage marasa matuƙa na Turkiyya, Baykar Technologies da lambobin yabo na ƙasar Mali saboda gudunmawar da suke bayarwa da ayyukan da suke yi a ƙasar da ke Yammacin Afirka.

An bai wa tawagar mai mutum huɗu, ƙarƙashin jagorancin shugabannin kamfanin Selcuk Bayraktar da Haluk Bayraktar lambar yabon ne a ranar Laraba.

Lambobin yabon su ne mafiya girma na karramawa a ƙasar, kuma an ba su su ne a wani taro da aka yi a fadar shugaban ƙasa, wanda ya samu halartar Ministan Tsaro na Mali Kanal Sadio Camara.

Tawagar ta kamfanin Baykar ta kuma gana da Shugaban Gwamnatin Riƙon Ƙwarya na Mali, Assimi Goïta.

“Mun ji daɗin karramawar da aka yi mana sosai wacce za ta sake ƙarfafa dangantaka da hadin kai tsakanin Turkiyya da Mali,” a cewar Haluk Bayraktar a wani saƙo da ya wallafa.

Ana karrama shugabannin ƙasashen waje da lambar yabon a matsayin wata alama ta ƙawance, da kuma waɗanda suka taimaka wajen ci gaban ƙasar.

A bara ne Mali da Turkiyya suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin kai a fannin soji da tsaro.

Bayraktar babban kamfani ne na Turkiyya mai ƙera kayayyakin soji da ke aiki a faɗin duniya, inda yake samun kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen shiga daga fitar da kayayyakin da yake yi.

A watan Afrilu ma, an bai wa shugaban kamfanin Baykar lambar yabo ta ƙasar a Burkina Faso. Hoto: Others

A watan Afrilu ma, an bai wa shugaban kamfanin Baykar lambar yabo ta ƙasar a Burkina Faso, inda aka shigar da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Bayraktar TB2.

Shi ma Haluk Bayraktar an ba shi lambar yabo ta Ordre de L'etalon Officier, wacce ita ce mafi ƙololuwar lambar yabo ta ƙasar, wacce shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya ba shi saboda gudunmawar da yake bai wa zaman lafiyar ƙasar da tsaro da ayyukan yaƙi da ta’addanci.

Bayraktar babban kamfani ne na Turkiyya mai ƙera kayayyakin soji da ke aiki a faɗin duniya. Hoto: (Getty Images).

Turkiyya ta kuma sayar wa wasu ƙasashen Afirka uku da suka haɗa da Maroko da Tunisiya da Habasha jiragen yaƙi marasa matuƙan. Sannan Nijar ma ta nuna sha’awarta ta mallakar jiragen yaƙi marasa matuƙa na TB2 Bayraktar.

TRT Afrika