An kama wani jirgin saman kasar Kenya a kan hanyarsa ta zuwa London a ranar Alhamis da rana, aka juya akalarsa yana tsaka da tafiya a sama, minti 45 kafin lokacin da aka saka na saukarsa a filin jirgin saman Heathrow.
"Kamfanin Jiragen Sama na Kenya Airways (KQ) ya tabbatar da cewa a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 10:30 na safe, hedikwatar kamfanin jiragen sama na Kenya ta samu saƙon cewa akwai wani lamari da ka iya zama barazanar tsaro a jirgin mai lamba KQ100 da ya tashi daga birnin Nairobi zuwa filin jirgin sama Heathrow na London," kamar yadda kamfanin jiragen saman na Kenya ya faɗa a wata sanarwa.
KQ ya ce gwamnatocin Kenya da na Birtaniya suna gudanar da "cikakken bincike a kan wannan barazanar."
"An yi wa ma'aikatan cikin jirgin bayani, kuma an ɗauki dukkan matakan tsaro da na kiyayewa don tabbatar da kare fasinjojin cikin jirgin," kamfanin na KQ ya ƙara da cewa.
'Yan sanda sun tabbatar da cewa za a yi bincike
Da misalin ƙarfe 3:45 agogon GME, an karkata saukar jirgin samfurin Boeing 787 a filin jirgin sama na Stansted da ke London, mai nisan kilomita 100 daga filin jirgin saman Heathrow na London.
'Yan sandan Essex sun ce a wata sanarwa a shafin X, suna "duba wani lamari a filin jirgin saman Stansted."
"An karkata wani jirgi da ke kan hanyar Heathrow daga Nairobi, zuwa filin jirgin Stansted da ranar yau, ƴan sandan Essex suka fada a ranar Alhamis da ƙarfe 4:35 na yamma agogon GMT.
Rahotanni sun ce an kama jirgin na KQ ne a lokacin da yake wucewa a sararin samaniyar ƙasar Faransa.
Marie Merrit, wanda ke cikin jirgin na KQ plane, ya rubuta a Facebook cewa "Saura minti 45 mu sauka a filin jirgin sama na Heathrow, sai aka ce mana an karkata mu zuwa filin jirgi na Stansted.
"Da muka sauka a Stansted sai muka ga motocin ƴan sanda da yawa. 'Yan sanda sun zagaye mu dukkan su sanye cikin kakinsu riƙe da bindigogi. Matuƙin jirgin bai ce ko uffan ba."
An katse sadarwa
Ma'aikatar Tsaro ta Birtaniya ta ce jirgin na kamfanin KQ "bai gamu da katsewar sadarwa ba, kuma an raka shi har filin jirgi na Stansted inda ya sauka lami lafiya. A yanzu haka dai hukumomi suna shawo kan lamarin."
Jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Birtaniya RAF ce kama jirgin, kamar yadda jaridar The Guardian ta rawaito.