Hukumar Sadarwa ta Kasar Ghana (NCA) ta yi gargadin cewa yin rajistar layin SIM fiye da guda daya da kuma ba da shi haya ga wani mutum, musamman ga baki da ke zuwa ziyara kasar ya sabawa doka.
A sanarwa da hukumar NCA ta fitar, ta ce an janyo hankalinta ne game da yadda wasu daidaikun mutane da hukumomi ke ba da hayar layin SIM ga baki da ke zuwa kasar daga kasashen waje har da wasu 'yan asalin kasar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.
Sanarwar ta ce tsarin ya sabawa dokar sadarwa ta 2016 da aka yi kwaskwarima a kasar.
“Hukumar NCA na son bayyana wa al'umma karara cewa daidaikun mutane da ma'aikatun da ke gudanar da irin wadannan ayyuka ba su samu izini daga hukumar ba.
Tsarin kasuwancinsu ya sabawa sashi 73b (1) na dokar sadarwa ta 2016 da aka yi wa gyara, wadda ta ce, ''Mutum ba zai yi mu'amala da tsarin shaidar abokin cinikinsa da aka riga aka yi masa rajista ba ko mai amfani da bayanansa ba".
Hukumar ta kara da cewa, tsarin ya saba wa manufar gudanar da aikin rajistar SIM na kasar, da ke bukatar hada duk bayani da shaidar mutum cikin katin SIM guda daya, don dakile miyagun ayyuka da kuma kiyaye bayanan sirri mutum.
“Kazalika, bin irin wannan tsari na nufin dokar kariya ta bayanai da ake son cimma ba zai yiwu ba, sannan masu amfani da layukan waya na SIM suna iya fuskantar hadari sakamakon yiwuwar wanda zai yi amfani da layin a gaba ya samu damar kutsawa cikin bayanan tsohon wanda ya yi amfani da layin a baya.
Hukumar ta ce wannan tsarin na ba da damar satar bayanan sirri musamman layin da aka ba da hayarsa, la'akari kan cewa suna daban aka yi amfani wajen rajistar SIM din kuma wani mai suna daban ke amfani da shi.
NCA ta gargadi masu gudanar da irin wannan tsarin da su gaggauta bari, kazalika hukumar ta gargadi 'yan kasar da baki da ke shigowa da su daina karfafa wa masu gudanar da wannan sana'a gwiwa ko kuma su fuskanci hadarin hukuncin da sashe na 73b (2) na dokar sadarwa ta 2016 da aka yi gyara ya gindaya.
Sanarwar NCA dai ta bukaci duk masu amfani da layin SIM da su bi tsarin da aka amince da shi na amfani da katin Ghana na shaidar dan kasa da wanda ba dan kasa ba ko fasfo ga baki don mallakar layin SIM a kasar.