Masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnati ta samar musu da tsaro. / Hoto: Dikko Radda

Mazauna Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina sun rufe wasu manyan hanyoyin jihar a ranar Asabar inda suke zanga-zanga saboda rashin tsaro.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun addabe su, haka kuma rayuwarsu tana ƙara taɓarɓarewa wanda hakan ya sa suka fito zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun yi kira da gwamnatin ƙasar ta tashi tsaye domin ta ba su tsaro sakamakon yadda abubuwa ke faruwa.

Masu zanga-zangar sun rufe hanyar Marabar-Kankara zuwa Katsina da kuma hanyar Malumfashi zuwa Funtua.

Jama’ar sun bayyana cewa za su ci gaba da rufe waɗannan hanyoyi idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba.

“A yanzu haka akwai gawarwakin jama’ar da ɓarayin daji suka kashe a cikin daji, kuma sun hana mu ɗauko gawarwakin.

“An yi kashe-kashe kwanaki uku da suka gabata. Abin da ke faruwa kenan a al’ummarmu a kullum,” kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito wani mai zanga-zangar yana cewa.

“Sun addabe mu, sun hana mu noma, abin da mutum zai ci a cikinsa babu,” kamar yadda masu zanga-zangar suka bayyana.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da matsanancin rashin tsaro.

Ko a watan Yunin da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka kashe mutum 26 a Gidan Boka da ke Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.

Haka kuma a watan Yunin ‘yan bindigar sun sake kashe wasu mutum bakwai a ƙauyen Mai Dabino da ke Ƙaramar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

TRT Afrika