Kusan wata biyar kenan Nijar din na fama da takunkumin da ECOWAS ta saka mata. / Hoto: TRT Afrika

Daruruwan yan kasar Nijar sun gudanar da tattaki tare da gangami a kusa da sansanin sojin kasar a jajibirin taron kungiyar ECOWAS wanda za a gudanar a ranar Lahadi a Abuja.

Tattakin wanda aka gudanar a birnin Yamai ya samu halartar wasu daga cikin jami’an gwamnatin mulkin sojin Nijar inda suka rinka furta kalamai na suka ga kungiyar ta ECOWAS.

Mahalarta gangamin sun yi ta sukar kungiyar ECOWAS dangane da takunkumin da ta saka wa Nijar. / Hoto: TRT Afrika

Mahalarta gangamin sun bukaci sojojin da ke mulki a Nijar kan cewa Nijar din ta gaggauta ficewa daga ECOWAS idan kungiyar ba ta yi sassauci kan takunkuman da ta saka ba a yayin taron da za ta gudanar a ranar Lahadi a Abuja.

A yayin da yake jawabi a madadin gwamnatin sojin Nijar, Kanal Ibro ya jinjina wa ‘yan kasar Nijar dangane da yadda suka bai wa sojojin kasar goyon baya tare da rokonsu kan cewa su kwantar da hankalinsu.

Sojojin na Nijar sun yi jawabi a yayin gangamin tare da gode wa 'yan kasar dangane da goyon bayan da suke ba su. / Hoto: TRT Afrika

Gangamin ya kuma samu halartar wasu daga cikin ‘yan fim din Hausa daga Jihar Kano da ke Nijeriya domin taya ‘yan Nijar din gangamin.

ECOWAS ta saka wa Nijar din takunkumi tun bayan da aka gudanar da juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Daga cikin takunkuman har da katse wutar lantarki da makwabciyar Nijar din Nijeriya ta yi tsawon watanni.

TRT Afrika