An fara taron yaƙi da wariyar launin fata na farko ga Falasdinu a Afirka ta Kudu

An fara taron yaƙi da wariyar launin fata na farko ga Falasdinu a Afirka ta Kudu

Masu jawabai sun yi Allah wadai da abin da ke faruwa a Falasdinu suna cewa zalunci ne na duniya kan al'ummar yankin.
Ministar Harkokin Wajen kasar Naledi Pandor ce ta gabatar da jawabin bude taron a madadin Shugaba Cyril Ramaphosa. Hoto / Dirco

Kasar Afirka ta Kudu na karɓar baƙuncin taron yaƙi da wariyar launin fata na farko na duniya ga Falasdinu, da nufin fayyace yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza da batun Falasɗinawa 'yan kama wuri zauna da mulkin mallaka da kuma sauran batutuwa.

Taron na kwanaki uku ya fara ranar Juma'a a Cibiyar Taro ta Sandton da ke Johannesburg, kuma ya jawo hankalin masu bayani daga ƙasashen duniya.

Waɗanda suka halarci taron sun hada da, Declan Kearney shugaban jam'iyyar siyasa ta kasar Ireland Sinn Fein da Mustafa Barghouti, ɗan fafutukar kare hakkin dan'adam kuma ɗan siyasa, da dai sauransu.

“Ba za mu yafe abin da ya faru da Falasdinawa ba. Tauye hakkin Falasdinawa da ake yi. Ba sa bari Falasdinawa su binne ‘yan'uwansu,” in ji Mustafa Barghouti a wurin taron.

Rashin adalcin duniya

Barghouti ya ce abin da ke faruwa a Falasdinu zalunci ne na duniya kan al'ummarta.

"Abin da muke fuskanta ba wai kawai wariyar launin fata ba ne, wani mummunan shiri ne na tsarin Isra'ila na ruguza Falasdinu. Kashi 70% na al'ummar Falasdinu sun rasa matsugunansu," in ji shi.

Ya ce kamata ya yi duniya ta tambayi me ya sa ba a amfani da dokokin kasa da kasa da hakkokin bil'adama a yayin yakin da Isra'ila ke ci gaba da yaƙi a Gaza da sauran rikice-rikicen duniya.

Ya ce Falasdinawa ba za su bar ƙasarsu ba, ba za su miƙa wuya ba, ko kuma su yi ƙasa a gwiwa.

Shari'ar Kotun ICJ

Barghouti ya kuma gode wa Afirka ta Kudu da ta tsaya tare da al'ummar Falasdinu da ake zalunta ta hanyar kai Isra'ila gaban kotun ƙasa da ƙasa ta ICJ, inda ake zargin Isra'ila da aikata kisan ƙare dangi.

Hukuncin wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya ce yana da kyau a ce Tel Aviv na aikata kisan kiyashi a yankin Gazan da ke gaɓar teku, ya kuma umurci Tel Aviv da ta dakatar da wannan aika-aika tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jinƙai ga fararen hula.

Kearney ya ce ba a taɓa ganin irin hadin kan da ake nuna wa talakawan Falasdinu a fadin duniya ba, kuma ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar Kotun ICJ a kan Isra'ila "abar ƙarfafa gwiwa ce."

Ya ce Isra'ila ba za ta taɓa karya ruhin gwagwarmayar Falasdinawa ba, yana mai cewa: "Muna tare da al'ummar Falasdinu a kan doguwar tafiyarsu ta neman 'yanci kuma ba za mu taba yin watsi da su ba."

TRT Afrika