Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai amince jami'an tsaron kasar su dinga zaman 'yan marina ba, inda ya nemi dukkan hukumomin tsaro da su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a ganawar da ya yi da shugabannin rundunonin tsaron kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.
A karshen taron wanda shi ne na farko da ya yi da jami'an tun bayan shan rantsuwa, shugaban kasar ya bayyana hanyoyin da zai bi wajen magance matsalolin tsaro, wadanda suka hada da bin matakan tsaro na zamani don inganta tsaron Nijeriya.
Bayan kammala taron, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno, wanda shi ne ya isar da sakon shugaban kasar, ya bayyana cewa Tinubu ya bukaci ganawa akai-akai da su don duba bukatun kasar, kuma zai aiwatar da sauye-sauye da dama.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa shugaban kasar ya kuma bai wa hukumomin tsaro umarnin fitar da wani tsari na yadda za a magance matsalolin satar danyen fetur.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanal Janar Farouk Yahaya da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Isiaka Amao da Babban Sifeton 'Yan sanda, Usman Alkali Baba.
Sai kuma Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS Yusuf Bichi da kuma Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.