An daure dan takarar shugaban kasa shekara bakwai a gidan yari kan cin mutuncin shugaban kasa

An daure dan takarar shugaban kasa shekara bakwai a gidan yari kan cin mutuncin shugaban kasa

Lauyan dan takarar ya ce "wannan matakin ya yi tsauri sosai musamman da yake babu damar daukaka kara.
Fadar shugaban kasa Felix Tshisekedi ta ce ba hannunta a hukuncin kotu. Hoto: AA

Wata babbar kotu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta yanke wa dan takarar shugaban kasar Jean-Marc Kabund hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari bisa laifi 12 da suka hada da yada jita-jita da cin mutuncin shugaban kasa, a cewar lauyansa a ranar Laraba.

Kabund tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki ne kuma na hannun daman Shugaba Felix Tshisekedi, wanda ya kaddamar da tasa jam'iyyar siyasar bara bayan shan kaye sau biyu.

Tun a watan Agustan 2022 da aka kama shi yake tsare a babban gidan yarin Kinshasa, bayan da ya kira Shugaba Tshisekedi da cewa shi din "masifa ne" tare da yin kaca-kaca da gwamnatinsa a wani jawabi.

"Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara hudu kan kowane laifi a laifuka tara na farko da kuma wata 16 a kowane laifi kan sauran laifuka ukun," kamar yadda lauyan Kabund Kadi Diko ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya ce mafi girman laifukan shi ne na "yada jita-jita" da kuma "cin mutuncin shugaban kasa da majalisar dokoki."

Lauyan ya kara da cewa "wannan matakin ya yi tsauri sosai musamman da yake babu damar daukaka kara.|

'Kasa na cikin gagarumar masifa'

Kabund bai halarci kotun ba lokacin da aka yanke hukuncin, amma a sauraron karar da aka yi a watan jiya, ya kare kansa tare da maimaita kalamansa.

"Na cewa mutane su yi duk abin da za su iya don tabbatar da cewa Mr Tshisekedi bai samu shiga takarar zabe mai zuwa ba, saoda na yi amannar cewa kasar na cikin masifa sosai a karkashin mulkinsa," kamar yadda ya shaida wa Babbar Kotun a watan Agusta.

Ana sa ran za a yi babban zabe a Congo ranar 20 ga watan Disamba inda ake ganin Tshisekedi zai iya neman tazarce karo na biyu. Al'amura suna sake daukar zafi a fagen siyasa tun kafin zaben.

A watan Yuli ne aka kashe wani dan jam'iyyar hamayya a babban birnin kasar, Kinshasa, yayin da jam'iyyun adawa suke gudanar da jerin zanga-zanga masu muni na yin tur da abubuwan "son rai" da aka gudanar a lokacin rajistar zabe.

'Ba hannun fadar shugaban kasa'

Babbar Kotu wadda tana daya daga cikin manyan kotunan Congo na koli ce ta yanke wa Kabund hukunci kan samunsa da laifi, inda ba shi da damar daukaka kara.

Ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a matsayinsa na shugaban jam'iyyar kawance ta "Alliance for Change" a zabe mai zuwa.

Mai magana da yawun Shugaban Tshisekedi, Tina Salama ta ce babu abin da ya shafi fadar shugaban kasa da sa baki a hukuncin kotu."

Reuters