Akalla mutum 14 ne suka mutu a Gabashin Ituri da ke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo bayan masu tayar da kayar baya sun kai hari wani coci a yayin da mabiya ke ibada, a cewar wani jami'i da kuma shugaban wata kungiyar fararen-hula.
Kungiyar Hadin Kai Don Ci gaban Congo wato (CODECO), daya daga cikin kungiyoyin mayakan sa-kai a gabashin kasar ce ta kai harin na ranar Lahadi, a cewar shugaban yankin Djugu, Ruphin Mapela da kuma shugaban kungiyar farar-hula ta Dieudonne Lossa a ranar Litinin.
"Mutanen da harin ya rutsa da su suna addu'a ne ga ubangijinsu a lokacin, amma saboda rashin tausayi maharan nan da aka gane cewa 'yan kungiyar CODECO ne suka bude musu wuta," in ji Lossa.
Dukkansu sun ce fararen-hula tara da maharan hudu da kuma wani soja daya ne suka mutu a harin.
Mapela ya ce maharan sun kai harin ne a cocin Mesa da Cepac da Aumopro da ke kusa da gabar Tafkin Albert a yankin masarautar Bahema-Nord.
"Muna kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu a yayin da dakarun soji suke neman maharan don daukar matakin da ya dace a kansu," a cewar kakakin rundunar sojin Ituri, Jules Ngongo Tshikudi.
CODECO tana ikirarin kare muradun manoman Lendu ne, wadanda suka dade suna fada da makiyayan Hema.
Hare-haren da kungiyar CODECO ke kai wa sun munana yanayin jinkai da aka dade ana fama da shi a yankin Ituri, inda mutum miliyan uku ke cikin tsananin bukatar taimako, a cewar hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.