Dakarun kawancen gabashin Afirka sun kwace iko da garin Bunagana, mai matukar muhimmanci a Jumhuryar Dimukradiyyar Kongo wanda mayakan M23 suke rike da shi sama da tsawon wata tara.
Kakakin Rundunar Kyaftin Ahmad Hassan ya sanar da cewa an kai sojojin Uganda garin Bunagana, za su kasance a garin sannan su bai wa mayakan M23 kofar ficewa daga cikinsa.
Ya ce “Mun yaba da umarnin M23 da yadda suka bayar da kai bori ya hau wajen ba mu kofar wucewa da kuma ba mu damar karbe iko da Bunagana.”
Mayakan na M23 ba su bayar da amsar tambayar ko sun fita daga Bunagana ko akasin haka ba.
Bukatar neman mayakan su bar Bunagana ta kasance a kan gaba a tattaunawa da dama da aka yi game da rikicin na DRC, inda sama da kungiyoyi masu dauke da makamai 120 suke rikici da juna saboda filaye da gonaki da mulki da albarkatun kasa da kare muhallansu.
TRT World