An cimma matsaya kan yarjejeniyar tsagaita wuta wadda za ta soma aiki daga ranar 4 ga watan Agustan bana a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) a ranar Talata.
Matakin ya biyo bayan wata tatattauna da ta gudana tsakanin DRC da Rwanda, kamar yadda fadar shugaban Angola wadda ke shiga tsakani a tattaunawar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar dai ba ta fayyace ɓangarorin da suka amince da tsagaita wutar ba, da kuma tsawon lokacin da yarjejeniyar za ta ɗauka ba.
A farkon watan Yuli ne aka tsagaita wuta na makonni biyu don kai agaji a yayin da ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnatin Congo da 'yan tawayen ƙungiyar M23.
Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu
Kongo dai na zargin Rwanda da mara wa kungiyar M23 baya, batun da Rwandan ta musanta.
Yaƙin da ake gwabzawa a lardin Kivu ta Arewa ya raba mutane fiye da miliyan 1.7 da muhallinsu, adadin da ya ƙara ninka mutanen da suka rasa matsugunansu a Congo sakamakon rikice-rikice da dama zuwa mutum miliyan 7.2, a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Congo ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa babu lokacin kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wutar.