Akasarin waɗanda aka ceto sun fito ne daga Jihar Kano. / Hoto: Abike Dabiri

Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya da ke Ƙasashen Waje NIDCOM ta ce an ceto mata da ƙananan yara 58 waɗanda aka yi safarar su zuwa Ghana kuma akasarinsu ‘yan Jihar Kano ne.

Shugabar hukumar ta NIDCOM Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar.

A sanarwar da ta fitar, ta ce hukumar ta yi nasarar ceto ƙarin mata da yara 58 wanda hakan ya kawo jumullar waɗanda aka ceto daga Accra babban birnin Ghana zuwa 105 a cikin wata uku.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bayar da ƙididdigar mutanen 58 waɗanda aka ceto inda ta ce akasarinsu ‘yan Jihar Kano ne.

Mutum 47 sun fito ne daga Jihar Kano sai biyar sun fito ne daga Katsina sai huɗu sun fito daga Kaduna sai biyu daga Jigawa, kamar yadda hukumar NIDCOM ta tabbatar.

Hukumar ta bayyana cewa tuni aka kama wasu waɗanda ake zargi da safarar matan da yaran inda aka miƙa su ga jami’an tsaro da kuma hukumar NAPTIP wadda ke da alhakin daƙile safarar mutane a Nijeriya.

Ko a watan Yunin da ya gabata sai da hukumar ta NIDCOM ɗin ta tabbatar da ceto mata 13 waɗanda aka yi safarar su zuwa Ghana.

TRT Afrika