Rundunar jami'an tsaro ta jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Nijeriya ta bankado wani kamfanin sarrafa magungunan jabu da ke aiki a jihohi 13 na kasar, mai suna Brother Paul Legacy Foundation.
Jami'an sun yi nasarar kama jabun magungunan da kamfanin yake hadawa da kuma sayar wa al'umma ne bayan samun labarin ayyukan da yake gudanarwa a ofishinsa da ke garin Akure babban jihar Ondo.
Babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya ta jihar Mrs. Folukemi Aladenola ta ce an kama wasu hade-haden magani da kamfanin ke sayar wa al'umma, wanda ya yi ikirarin yana magance duk wata cuta da ke damun dan'adam.
Kazalika Aladenola ta ce kamfanin na gudanar da irin wannan sana'a a jihohi 13 da ke Nijeriya ciki har da Ondo.
Aladenola ta shaida wa manema labarai cewa “Tun a watan Yuli muka samu labarin cewa tawagar jami'an kamfanin ta shigo gari, wadanda suke rudar mutane cewa maganinsu na warkar da kowace irin cuta, kama da daga ciwon daji da ciwon suga da hawan jini da ciwon hanta da kuma rashin haihuwa a tsakanin mata da dai sauransu cikin farashi mai rahusa, sannan sun yi ikirarin hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta yi wa kamfaninsu rajista.''
NAFDAC ta karyata bayanan kamfanin, inda wakilin hukumar Mr. Samuel Olatunji ya bayyana cewa ikirarin kamfanin na mallakar lambar rajista daga gare su ba gaskiya ba ne.
A cewar Mrs. Aladenola, gwamnatin jihar Ondo ta yi kokari wajen tabbatar da cewa al’ummarta sun samu hanyoyin samun lafiya cikin sauki inda ta samar da cibiyoyin kiwon lafiya a wadace da kuma dakatar da biyan kudin yin rajista a dukkanin cibiyoyin gwamnati na jihar don rage radadin illar cire tallafin man fetur da gwamnatin tarrayar kasar ta yi.
“Ya kamata mutane su yi amfani da wannan dama da gwamnati ta bayar wajen zuwa duba lafiyarsu a asibitocin gwamnati, amma abin takaici har yanzu mutane na biye wa ire-iren mutanen da ba su da kwarewa, suna karbar Naira 5,000 zuwa 10,000 daga hannunsu," in ji Aladenola.
Aladenola ta shawarci al’umma jihar da su yi kokari wajen ziyartar kwararrun da cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu tare da jaddada cewa za a mika kamfanin ga hukumar da ta dace don fustantar hukunci.
Shugaban rundunar tsaro ta Task Froce na jihar Ondo, Olugbenga Lasekan, ya gargadi masu saya da kuma shan jabun magunguna da su kaurace wa yin hakan tare da jaddada cewa hukunci zai hau kan duk wanda aka kama da aikata laifi.