Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta tabbatar da barkewar Cutar Makarau ta Diphtheria a kasar inda ta ce ya zuwa yanzu mutum 80 ne suka mutu.
A sanarwar da NCDC ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ya zuwa ranar 30 ga watan Yuni a kalla mutum 798 ne suka kamu da cutar.
Sanarwar ta ce tun bayan barkewar cutar a watan Disambar 2022, ta samu rahoton bullar cutar da dama a wasu jihohi da ke fadin kasar.
“Ya zuwa 30 ga watan Yuni 2023 an tabbatar da mutum 798 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 cikin jihohi takwas ciki har da babban birnin kasar Abuja,’’ in ji sanarwar.
Sanarwar hukumar ta kara da cewa Jihar Kano ita ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar da mutum (782), sai kuma jihohin Legas da Yobe da Katsina da Cross Ribas da Kaduna da kuma jihar Osun da aka samu barkewar cutar.
Kazalika kashi 71.7 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar yara ne ‘yan tsakanin shekara biyu zuwa 14, kuma ya zuwa yanzu mutum 80 ne suka mutu daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, a cewar sanarwar.
Cutar makarau dai cuta ce da kwayoyin cutar bakteriya mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta. Wacce ke shafar hanci da makogwaro, da kuma wani lokacin, fatar mutum.
Ta fi kama yara kananan da manyan mutane musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.
Wasu daga cikin alamomin cutar sun hada da zazzabi da yoyon hanci da tari da kuma ciwon makogwaron sannan idanun mutum za su yi jajawur da kuma kumburin wuya.
Don dakile yaduwar cutar a Nijeriyya Hukumar NCDC, ta ba da shawara kan ana yi wa yara rigakafin cutar (rigakafi mai dauke da sinadarin diphtheria toxoid) har sau uku tun suna sati shida da goma da kuma 14 da haihuwarsu.