NAFDAC ta ce ana shiga da sukarin ta iyakokin kasar daban-daban

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta gargadi ‘yan Nijeriya kan wani nau’in sukari wanda ake shiga da shi kasar daga Indiya da Brazil.

Hukumar ta ce wannan sukarin ba ta yi masa rajista ba kuma ba ya dauke da sinadarin Vitamin A.

A sanarwar da hukumar NAFDAC ta fitar, ta bayyana cewa wannan nau’in na sukarin barazana ne ga lafiyar masu amfani da shi.

Sukarin ana shiga da shi ne ta Nijeriya ta kan iyakokin kasar da suka hada da Kamaru (Douala) da Nijar da Chad da Jamhuriyyar Benin ta iyakokin Borno da Adamawa da Legas da Oyo da Ogun.

Hukumar ta NAFDAC ta ce ta gano cewa a duk wata kusan tirela 200 na sukarin ake sayarwa a kasuwannin Nijeriya da ke Mubi da Gamboru’gala da Saki da Keshi da Badagry da Idi – Iroko, haka kuma ana sayar da duk buhu tsakanin N32,000 zuwa N34,000.

Hukumar ta NAFDAC ta bukaci masu shigar da sukarin cikin kasar da ‘yan sari da masu shaguna da masu siya kan nisantar wannan nau’i na sukari.

Ko a ‘yan kwanakin nan sai da hukuamr ta NAFDAC ta gargadi ‘yan kasar kan su yi taka tsantsan wajen shan wani gurbataccen lemon kwalba na Sprite mai yawan 50cl da ya watsu a kasar.

TRT Afrika